Dubu Ta Cika: Rikakken Dan Bindiga Ya Shiga Hannu bayan Shekara 11 Ana Nemansa

Dubu Ta Cika: Rikakken Dan Bindiga Ya Shiga Hannu bayan Shekara 11 Ana Nemansa

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake nema ruwa a jallo
  • Kakakin rundunar ya bayyana cewa an cafke ɗan bindigan ne a ƙaramar hukumar Giwa bayan kwashe dogon lokaci ana nemansa
  • DSP Mansir Hassan ya bayyana cewa an samu makamai a hannun ɗan bindiganai suna Mati Bagio

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta cafke wani da ake zargi da zama jagoran ƴan bindiga mai suna Mati Bagio, mai shekaru 34 da haihuwa.

Rundunar ƴan sandan ta cafke tantirin ɗan bindigan ne bayan shekara 11 jami'an tsaro suna farautarsa

'Yan sanda sun cafke dan bindiga a Kaduna
'Yan sanda sun kama rikakken dan bindiga a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Riƙaƙƙen ɗan bindiga ya shiga hannu

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Zamfara, an samu asarar rayuka

Kakakin ƴan sandan ya ce an kama wanda ake zargin ne a Unguwar Galadima da ke cikin yankin Shika a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Tun shekara 11 da suka wuce, Mati Bagio na cikin jerin waɗanda rundunar ke nema ruwa a jallo bisa jagorantar ƙungiyar ƴan ta’adda da ke addabar al’ummomi a jihohin Kaduna da Katsina.

Bisa bayanan da ƴan sanda suka bayar, an ce Mati Bagio ya jagoranci hare-hare da dama a yankunan Giwa, Hunkuyi, Faskari, Dandume da Funtua kafin daga ƙarshe a kama shi.

Sanarwar ta bayyana cewa, yayin da aka cafke shi, ƴan sanda sun ƙwato muggan makamai iri-iri, harsasai, wata mota kirar Toyota Prado da kuma babura guda biyu da ake zargin an sace su, rahoton TheCable ya tabbatar.

"A ranar 18 ga Yuli, 2025, da misalin ƙarfe 05:30 na safe, bisa sahihan bayanan leƙen asiri, tawagar ƴan sanda ƙarƙashin jagorancin shugaban sashen yaƙi da garkuwa da mutane, CSP Sani Zuntu."
"Ta yi nasarar bin sawu tare da cafke wani sanannen shugaban ƴan ta’adda da aka fi sani da Mati Bagio, ɗan shekara 34, mazaunin Unguwar Galadima a yankin Shika, ƙaramar hukumar Giwa, Jihar Kaduna."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an tafka barna

“Wanda ake zargin sanannen jagoran ƴan bindiga ne da ya addabi jihohin Kaduna da Katsina ta hanyar kai hare-hare a Giwa, Hunkuyi, Faskari, Dandume da Funtua."
"Ya daɗe yana guje wa hukuma na tsawon shekara 11. An cafke shi a gidansa inda aka gano manyan makamai da harsasai masu tarin yawa."

- DSP Mansir Hassan

Rikakken dan bindiga ya shiga hannu a Kaduna
'Yan sanda sun kama rikakken dan bindiga a Kaduna Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga

Ƴan bindiga sun sace dabbobi a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a ƙaramar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Ƴan bindigan sun sace dabbobi masu yawa a harin da suka kai da safiyar ranar Juma'a a wani ƙauye.

Hakazalika, ƴan bindigan sun lalata motar ƴan sanda a wata musayar wuta da suka yi bayan sun yi musu kwanton ɓauna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng