Sheikh Pantami Ya Yi Kyautar ban Mamaki da aka Yi wa Buhari Takwara a Bauchi

Sheikh Pantami Ya Yi Kyautar ban Mamaki da aka Yi wa Buhari Takwara a Bauchi

  • Wani bawan Allah a Bauchi ya sanya wa dansa suna Muhammadu Buhari domin girmamawa ga tsohon shugaban kasa da ya rasu
  • Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya tura masa kyautar Naira 200,000 domin sayan rago don bikin suna
  • Malam Danladi Mai Kaset ya ce ya samu sakonni daga jihohi daban-daban da suka yaba masa, ya kuma roki Allah ya albarkaci jaririn

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Wani matashi mai suna Malam Danladi Mai Kaset daga jihar Bauchi ya yi abin da ya ja hankalin jama’a a kafafen sada zumunta.

Wannan kuwa ya faru ne bayan da ya bayyana cewa ya sanya wa jaririn da matarsa ta haifa suna Muhammadu Buhari.

Matashin da ya yi Buhari mai suna dauke da jaririn da aka haifa masa
Matashin da ya yi Buhari mai suna dauke da jaririn da aka haifa masa. Professor Isa Ali Pantami|Muhammad Sagir Ibrahim
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da Muhammad Sagir Ibrahim ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Ahmadu Yaro: Attajirin da ya shafe shekaru yana ba Buhari kudin cefane da sauransu

Danladi ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne domin girmama tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda Allah ya yi wa rasuwa kwanan nan a birnin Landan na Ingila.

Yayin da ake cikin jimamin rasuwar tsohon shugaban, ya ga ya dace ya karrama Muhammadu Buhari da yi masa takwara.

Dalilin yi wa shugaba Buhari takwara

Malam Danladi Mai Kaset ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin masu alfahari da irin gwagwarmayar da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a rayuwarsa ta shugabanci.

Ya ce ga shugaban ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen tabbatar da gaskiya da adalci a Najeriya. Shi yasa ya yanke shawarar sanya wa dansa da Allah ya azurtani da shi suna Muhammadu Buhari.

Danladi ya ce an haifi jaririn ne a lokacin da ake cikin jimamin rasuwar shugaban a Najeriya, kuma hakan ya kara masa kwarin gwiwa ya sanya masa wannan suna mai muhimmanci.

Kara karanta wannan

'Yadda Buhari ya yaƙi Bankin Duniya da IMF domin kare talakan Najeriya'

Shugaba Buhari da ya rasu a makon da ya wuce.
Shugaba Buhari da ya rasu a makon da ya wuce. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

Pantami ya aika da kyautar N200,000

Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, wanda ya yi aiki tare da marigayi shugaba Buhari, ya nuna jin dadinsa da wannan mataki da Danladi ya dauka.

Sheikh Pantami ya turo sakon kyautar Naira 200,000 ta hannun Malam Sham’un A. Damji domin Danladi ya yi amfani da su wajen sayan ragon suna.

Malam Danladi ya ce bai yi tsammanin hakan ba, kawai an aika masa da sakon cewa Sheikh Pantami ya turo masa da kyautar kudi saboda jin dadin wannan suna da ya sa.

Martanin Danladi bayan kyautar Pantami

Malam Danladi Mai Kaset ya ce yana mika godiyarsa ga Sheikh Pantami bisa karamcin da ya nuna masa.

Ya kara da cewa sakonnin da ya samu daga jihohi da dama kamar Kano da Taraba sun nuna masa cewa mutane da yawa sun yaba da abin da ya yi.

Matar da ta reni Buhari ta hadu da Pantami

Kara karanta wannan

Farfesa Pantami ya tuna kyaututtuka 2 da Buhari ya yi masa da ba zai taɓa mantawa ba

A wani rahoton, kun ji cewa Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya ziyarci wata dattijuwa a Daura.

Malamin ya bayyana cewa an ba shi labarin cewa matar ce ta yi rainon shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da ya ke karami.

Bayan sun gana da matar, Sheikh Isa Ali Pantami ya tabbatar da cewa ta ba shi kyautar Al-Kur'ani mai girma da darduma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng