Gaskiya Ta Ƙara Fitowa, An Ji Babban Abin da Ya Hana Buhari Korar Wasu Ministoci a Mulkinsa

Gaskiya Ta Ƙara Fitowa, An Ji Babban Abin da Ya Hana Buhari Korar Wasu Ministoci a Mulkinsa

  • Tsohon shugaban ma'aikatan faɗar shugaban ƙasa, Ibrahim Gambari ya ce Muhammadu Buhari na son ministocinsa kamar yadda yake son talakawa
  • Gambari ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Buhari ya gaza korar wasu ministoci da aka yi ta ce-ce-ku-ce a kansu ne saboda yana kaunarsu
  • Ya kuma tabbatar da cewa Buhari yana da waɗannan mutane masu ƙarfin faɗa a ji da ake kira 'cabal' a lokacin mulkinsa amma duk da haka sun san iyakarsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari, wasu daga cikin mutanen da suka yi aiki da shi na ci gaba da bayyana halayensa.

Tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana dalilin da ya sa Buhari bai kori wasu ministocinsa ba duk da koke-koke a kansu da kuma kiraye-kirayen da ake yi na yin waje da su.

Kara karanta wannan

An fara fito da bayanai kan 'cabal', Gambari ya fallasa yadda aka mamaye gwamnatin Buhari

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Gambari ya bayyana dalilin da ya sa ba a kori ministoci ba a gwamnatin Buhari Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

Gambari ya yi wannan bayani ne a wata hira da aka yi da shi a shirin ‘Inside Sources’ na Channels Television, wanda aka watsa a Abuja jiya,

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa Buhari ya gaza korar ministoci?

Farfesa Gambari ya bayyana marigayi Buhari a matsayin mutum mai tausayi wanda ya yiwa Najeriya hidima da duk abin da ke hannunsa.

A cewarsa, Shugaba Buhari bai sallami wasu daga cikin mukarrabansa ba ne domin yana ƙaunar su kamar yadda yake ƙaunar ‘yan Najeriya gaba ɗaya.

Gambari, wanda ya kasance wakili a Majalisar Ɗinkin Duniya a baya, ya rike matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa a wa’adin Buhari na biyu daga 13 ga Mayu, 2020 zuwa 29 ga Mayu, 2023, bayan rasuwar Abba Kyari.

Ya kuma bayyana yadda wasu muƙarrabai masu karfi da ake kira "cabal" suka rika tsallake shi suna mika takardu kai tsaye ga Buhari ba tare da sun bi ta ofishinsa ba.

Kara karanta wannan

'Mun gode,' kalaman yaran Buhari bayan jama'a sun yafe wa tsohon shugaban kasa

Yadda 'Cabal' suka mamaye gwamnatin Buhari

A rahoton Leadership, Gambari ya ce:

"Ana cewa akwai irin waɗannan mutane masu juya shugagan ƙasa, babu shakka akwai. Kowace gwamnati tana da irin nata gaggan masu ƙarfin juya gwamnati. Wasu suna kiransu da kitchen cabinet, wasu kuma think tank.
"Obasanjo yana da ƙungiya ta musamman da ke ba shi shawara, irin su Aboyade da sauransu. Wannan shi ne yanayin ofishin shugaban ƙasa, dole ya samu mutane a ciki da wajen gwamnati, da zai faɗa masu komai da yake so."
“Wasu daga cikin waɗannan mutanen suna da ƙarfi fiye da wasu, amma zan iya faɗa da ƙarfin gwiwa cewa kowace gwamnati tana da irin nata. Don haka, tabbas, akwai cabal a mulkin Buhari.”

Gambari ya ƙara da cewa duk da Buhari na da wasu mutane masu ƙarfi da ke tasiri wajen yanke shawarwari a mulki, amma sun san iyakarsu.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ibrahim Gambari ya tabbatar da cewa akwai jiga jigan da suka kewaye Buhari a gwamnatinsa Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Wani masoyin Buhari, Muhammad Ahmad ya shaidawa Legit Hausa cewa babu bukatar tuna komai game da marigayin, abin yake buƙata addu'a

Kara karanta wannan

Hakeem Baba: Dattijon Arewa ya tsage gaskiya kan 'kurakuran' Buhari

A cewarsa, kowa ya san Buhari mutumin kirki ne, don haka ya yi iya bakin ƙoƙarinsa a lokacin mulkinsa.

Ahmad ya ce:

"Ban cika son ana tono wasu abubuwan ba, fatanmu Allah Ya masa rahama, mutum ai tara yake bai cika 10 ba, kowa na kuskure, Allah Ya gafarta ma Baba Buhari."

Galadima ya tuna waɗanda suka taimaki Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa Buba Galadima ya bayyana cewa akwai mutane da dama da suka taimaka wa Muhammadu Buhari tun daga tushe, amma daga bisani aka watsar da su.

Ya ce su da suka hada gwiwa da Buhari tsawon shekaru don ganin ya kai ga mulki an mayar da su baya a gwamnatinsa.

Buba ya bayyana cewa Alhaji Ahmadu Yaro wanda aka fi sani da Coca-Cola ne ya rika ba Buhari albashi da kudin cefane har ya samu nasara a 2015.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262