Shin Allah Zai Yafewa Buhari ko da Al'umma ba Su Yafe Masa ba? Sheikh Ya Yi Bayani

Shin Allah Zai Yafewa Buhari ko da Al'umma ba Su Yafe Masa ba? Sheikh Ya Yi Bayani

  • Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi jawabi mai ratsa zuciya kan rasuwar Muhammadu Buhari, inda ya bukaci shugabanni su ji tsoron Allah
  • Ya soki malamai da ke cewa Allah SWT zai yafe wa Buhari duk da wasu ba su yafe masa ba, yana cewa hakan kuskure ne
  • Baristan ya bayyana cewa Allah ba zai yafe hakkin wani mutum ba sai wanda aka zalunta ya yafe ko kuma an biya shi hakkinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi magana mai kama hankali bayan rasuwar marigayi Muhammadu Buhari.

Barista Ishaq Adam ya soki wasu malamai da ke cewa ko al'umma ba su yafewa Buhari ba Allah zai yafe masa.

Sheikh ya yi magana bayan mutuwar Buhari
Sheikh ya yi bayani kan hakkin yan Najeriya kan Buhari. Hoto: Sheikh Ishaq Adam Kano, Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da shafin Daga Malamanmu ya wallafa a manhajar Facebook a jiya Juma'a 18 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

'Na yarda na yi kuskure': Sheikh Jingir ya ba da hakuri bayan sukar Malam Rigachukun

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rasuwar Buhari: Malami ya shawarci shugabanni

Batista Ishaq Adam ya ce babu inda Allah zai yafewa dan Adam hakkin wani da ke rataye a kansa.

Ya ce:

"Shugaba Muhammadu Buhari Allah ya jikansa da rahama, ya rasu, kuma lokacin da za a saka shi a kasa Tinubu yana wurin.
"Da zai yi hankali da tunani, a fada masa kamar yadda wannan ya zo ya gama shekara takwas ya kare a nan wurin.
"Kai ma za ka yi shekaru hudu ko takwas ka zo ka kare a nan wurin, don haka abin da za ka yi sai ka ji tsoron Allah."
Shehi ya shawarci shugabanni bayan rasuwar Buhari
Sheikh Ishaq Adam ya yi jawabi kan maganganu game da rasuwar Buhari. Hoto: Sheikh Barr. Ishaq Adam Ishaq.
Source: Facebook

Malami ya magantu kan yafiyar Allah a lahira

Malamin ya ce an yi ta tattaunawa bayan rasuwar marigayin yayin da wasu ke yafewa da kuma wadanda ba su yafe masa ba.

Ya kara da cewa:

"Bayan rasuwarsa aka zo ana tattaunawa, matar shugaban kasa ta ce a yafe masa, idan ka yafe masa ba ka yi laifi ba.

Kara karanta wannan

Ahmadu Yaro: Attajirin da ya shafe shekaru yana ba Buhari kudin cefane da sauransu

"Wasu malamai suka kai makura wai koma ba ka yafe masa ba Allah na iya yafe masa, bai kamata a ce malamai su rika fadan irin wannan ba.
"Dalili, za ka saka duk wanda ya samu ya yi zalunci da cewa Allah zai yafe masa, duk wani hakki a ranar karshe sai an dawowa da mai shi kafin mutum zai wuce.

Barista Ishaq ya ce idan abu tsakaninka da Allah yana iya yafewa amma hakkin wani dole sai ya yafe maka ko ka biya shi tun kafin a je lahira.

"Idan wani abu ne tsakaninka da Allah ne ka yi nadama ka tuba, amma malamai suka ce idan ya haɗa da hakkin wani sai ka je ya yafe maka ko ka biya shi."

- Cewar Sheikh Ishaq Adam Ishaq

Shehin malamin ya ba da misalin wani ya sace maka waya kawai daga baya domin ya tuba shikenan wayar ka ta tafi a banza?.

Malamin ya ce haka ba zai faru ba, Allah ba zai yafe maka ba har sai shi ya yafe maka ko ka biya shi.

Kara karanta wannan

Hakeem Baba: Dattijon Arewa ya tsage gaskiya kan 'kurakuran' Buhari

Rasuwar Buhari: Daurawa ya roki yan Najeriya

Mun ba ku labarin cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya roki ƴan Najeriya su sanya Muhammadu Buhari a addu'o'insu su kuma yafe masa kura-kuransa.

Kwamandan rundunar Hisbah ta Kano ya yi wannan roko ne yayin da ake jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasar a Najeriya.

A ranar Lahadi da ta gabata ne Allah ya karɓi ran Buhari, wanda ya shafe shekaru takwas yana mulkin Najeriya daga 2015 zuwa 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.