'Na Yarda na Yi Kuskure': Sheikh Jingir Ya ba da Hakuri bayan Sukar Malam Rigachukun

'Na Yarda na Yi Kuskure': Sheikh Jingir Ya ba da Hakuri bayan Sukar Malam Rigachukun

  • Sheikh Sani Yahaya Jingir ya fitar da sabon bidiyo na ba da hakuri kan kalaman da ya yi a wani wa’azi da ya jawo cece-kuce
  • Malamin ya ce wasu sun ce wa’azinsa ya yi zafi, amma suka tabbatar masa duk maganganunsa gaskiya ne, ba karya ba
  • Jingir ya nemi gafara daga wadanda kalamansa suka taba, inda ya yarda cewa hanyar da ya bi wajen fadar gaskiyar ta yi tsauri

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Shugaban kungiyar Izalah ɓangaren Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi sabon bidiyo na ba da hakuri.

Sheikh Jingir ya fitar da bidiyon ne bayan ce-ce-ku-ce a makon da ya gabata kan ziyarar Peter Obi a Kaduna.

Sheikh Jingir ya ba da hakuri kan kalamansa
Sheikh Jingir ya fitar da bidiyo na musamman bayan sukar Malam Rigachukun. Hoto: Hamza Muhammad Sani, Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachukun.
Source: Facebook

Peter Obi: Ana ta kiran Jingir kan kalamansa

Kara karanta wannan

Shin Allah zai yafewa Buhari ko da al'umma ba su yafe masa ba? Sheikh ya yi bayani

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Rabi'u B Goro ya wallafa a daren yau Juma'a 18 ga watan Yulin 2025 a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A faifan bidiyon, Sheikh Jingir ya ce an yi ta kiransa cewa maganganun da ya yi sun yi zafi zafi sosai.

Sai dai malamin ya yi tambaya cewa shin abin da ya fada gaskiya ne ko ba gaskiya ba.

A cewarsa:

"Ya kamata idan aka ce kana zafi to sai ka sassauta, amma fa ba in bar gaskiya ba.
"To gaskiya kaman mako daya ko biyu da ya wuce, na samu irin wadannan mafadan sun yi ca a kaina, suka ce wa'azinka na yau ya yi zafi.
"Na ce ya yi zafi? Suka ce eh, na ce akwai abin da na fadan da ba haka ba? Suka ce a'a duk maganar da ka fada gaskiya ce.
Sheikh Jingir ya nanata abin da ya fada kan Peter Obi
Sheikh Jingir ya fadi yadda ake ta kiransa kan kalaman da ya yi. Hoto: : JIBWIS Gombe.
Source: Facebook

Sheikh Jingir ya ba da hakuri kan kalamansa

Malam Sani Yahaya Jingir ya yi godiya ga Allah tun da abin da ya fada gaskiya sai dai kawai ya yi zafi a kalamansa.

Kara karanta wannan

'Shehu Dahiru Bauchi bai yarda Inyass na bayyana a jikin bango ko sama ba,'

Daga bisani ya ba da hakuri ga wadanda suka ji zafin abin da ya ce inda ya ce ya yarda ya yi kuskure.

Jingir ya kara da cewa:

"Na ce to Allah nagode maka, amma hanyar da ka bi ka fada ta yi tsanani, na ce to kamar meye na fada?
"Suka ce ka ce wawa, jahili, idan mutum ba mahaukaci ba ne ya za a yi a kashe Sardauna Kaduna a ba masu kashe shi wurin zama.
"Suka ce wadannan kalmomin sun yi zafi amma abin da ka fada haka ne, na ce abin da na fada haka ne? To na yarda na yi kuskure, duk abin da na fada da ya yi zafi, wanda ya yiwa zafin ina rokon ya yafe mani."

Malam ya shawarci Rigachukun bayan sukar Jingir

Kun ji cewa Sheikh Muhammad Nuru Khalid ya nuna damuwa da kalaman Sheikh Sani Jingir game da Malam Yusuf Sambo Rigachukun.

Sheikh ya ce malamai su ne matsalar Najeriya, idan aka gyara su komai zai daidaita, ya bukaci a daina jifan juna da kalmomin batanci.

Ya ce zargin Peter Obi da kisan Sardauna ba daidai ba ne, ya roki malamai da mabiyansu su guji tayar da fitina a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.