Yobe: Sarki Ya Tara Malamai, Sarakuna domin Addu'o'i na Musamman ga Buhari

Yobe: Sarki Ya Tara Malamai, Sarakuna domin Addu'o'i na Musamman ga Buhari

  • Sarkin Damaturu, Alhaji Shehu Hashimi II, ya tara manyan kasa da malamai domin addu'a ga Muhammadu Buhari
  • Sarkin ya jagoranci addu’o’in musamman domin rokon gafara da rahamar Allah ga marigayi Buhari da ya rasu a birnin London
  • Dubban malamai, masu mukaman gargajiya da al’umma sun halarci taron da aka shirya domin mutunta Buhari da kuma karrama shi da addu’o’i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Sarkin Damaturu, Alhaji Shehu Hashimi II Ibn Umar Al-Amin El-Kanemi, ya jagoranci addu'o'i ga marigayi Muhammadu Buhari.

Sarkin ya jagoranci addu’o’in musamman domin neman gafara da karrama marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

An yi addu'o'i ga Buhari bayan rasuwarsa
Sarkin Damarutu ya tara malamai domin addu'o'i ga Buhari. Hoto: Musa Dikko.
Source: Facebook

Rahoton NTA News ya ce an shirya addu’ar ne karkashin kulawar Majalisar Masarautar Damaturu da ke jihar Yobe a Arewa maso Gabas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rasuwar Buhari ta girgiza Tinubu, yan Najeriya

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai halarci taron addu'a da Allah Ya karɓi rayuwar Mai Martaba Sarki

Dukan wannan na zuwa ne bayan rasuwar tsohon shugaban kasar a birnin London a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025.

Shugaba Bola Tinubu da mukarrabansa da sauran manyan yan siyasa a Najeriya sun yi ta tura sakwannin ta'aziyya bayan rasuwar marigayin.

Dalilin haka ne ma, Tinubu ya ayyana ranar hutu domin birne marigayi a garin Daura da ke jihar Katsina ranar Talata 15 ga watan Yulin 2025.

An yi addu'o'i ga Buhari a Damaturu

Manyan malamai, masu mukamai da jama’a sun taru domin rokon rahamar Allah ga marigayi Buhari.

Sarkin, wanda shi ne shugaban Muminai na masarautar, ya bukaci daukacin shugabannin gargajiya da jama’ar masarautar su yi addu’ar gafara ga Buhari.

An gudanar da wannan addu’a ne bisa umarnin Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, wanda ya bayyana hutu domin bai wa jama’a damar yin addu’o’i.

An yabawa matakin Gwamna Buni a matsayin girmamawa, biyayya da nuna kima ga tsohon shugaban kasar Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari.

Malamai da sarakuna sun yiwa Buhari addu'o'i
Sarkin Damaturu ya jagoranci addu'o'i ga Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Sarki ya yabawa kyawawan halayen Buhari

Kara karanta wannan

"Ina kewarsa," Tinubu ya faɗi alaƙarsa da Ɗantata yayin ta'aziyya a Kano

A yayin taron, malamai sun karanta ayoyi daga Alkur’ani da yin addu’o’i domin neman rahama da gafara ga marigayi Buhari.

A cikin jawabinsa, Sarkin Damaturu ya yabawa Buhari bisa kaskantar da kai, gaskiya da gudunmawarsa wajen ci gaban Najeriya da rayuwa mai tsabta.

Ya kuma jinjinawa Gwamna Buni bisa irin jagoranci da tabbatar da jihar Yobe ta shiga cikin girmamawa da juyayin Buhari da mutunci.

Addu’ar ta musamman da aka gudanar a Damaturu ta nuna alhini da kaunar da ake yi wa Buhari, wanda ya shahara da gaskiya da kishin kasa.

An yiwa Buhari addu'o'i na musamman a Daura

Mun ba ku labarin cewa ana cigaba da yiwa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ruwan addu'o'in domin neman rahama da jin kai.

Majiyoyi sun ce manyan malamai na Musulmi da Kiristoci sun gudanar da addu’o’in neman rahama a Daura inda aka roki Allah ya gafartawa Buhari.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai fitattun malaman addinin Musulunci da na Kirista a ciki da wajen jihar Katsina.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.