'Mun Gode,' Kalaman Yaran Buhari bayan Jama'a Sun Yafe wa Tsohon Shugaban Kasa
- Wasu daga cikin yaran tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sun fara gode wa yan Najeriya da ke cewa sun yafe wa mahaifinsu
- Bayan rasuwar Muhammadu Buhari ne mutane da dama suka fito, suna ikirarin cewa ba sa neman hakkinsu a wajen tsohon shugaban
- Hanan da Hadiza Buhari, sun bayyana jin dadi a kan yadda 'yan Najeriya suka nuna soyayya ga mahaifinsu, tare da yi masu addu'a
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Har yanzu ana ci gaba da jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a fadin ƙasar.
Daya daga cikin abubuwan da suka ja hankali shi ne yadda jama'a da dama ke fito wa kafafen sada zumunta suna bayyana cewa sun yafe duk wani hakkinsu da ya rataya a wuyan tsohon shugaban.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta ƙara fitowa, an ji babban abin da ya hana Buhari korar wasu ministoci a mulkinsa

Source: Facebook
A hira da wasu daga cikin ‘ya ’yansa da BBC Hausa ta yi, an ji suna bayyana godiyarsu ga waɗanda suka yafe wa mahaifinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Ya’yan Buhari sun gode wa yan Najeriya
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Aisha Hanan Buhari da Hadiza Muhammadu Buhari, sun nuna farin cikinsu ga dukkannin mutanen da suka yafe wa mahaifinsu.
Marigayi Muhammadu Buhari ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan a ranar Lahadi, bayan fama da doguwar jinya.
Wadanda suka san shi sosai sun bayyana shi a matsayin mutum mai kirki, kishin kasa, da kaunar iyalinsa.
Hanan Buhari ta bayyana jimaminta
Hanan, wacce aka fi sani da Aisha Hanan Buhari, daya daga cikin ’ya’yan marigayin, ta bayyana yadda ta ji bayan rasuwar mahaifinta.
Ta bayyana cewa:
“Rasuwarsa kamar an yanke wani bangare na jikina ne. Abin da zan fi tuna da shi sosai shi ne barkwancinsa."
Ta ce suna godiya ga dukkannin ’yan Najeriya da suka yafe wa mahaifinsu bayan an samu labarin rasuwarsa.

Kara karanta wannan
Buhari, Sheikh Abubakar Gumi da wasu jagororin Najeriya 5 da suka rasu a birnin Landan
Ta ce:
“Ba mu da abin da za mu ce wa masu yafe masa sai dai mu ce, mun gode, Allah ya saka da alheri.”
Hadiza Buhari tana jimamin rashin mahaifinta
Hadiza Buhari, wacce ake yi wa lakabi da Nana, kuma ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayin daga tsohuwar matarsa, ta bayyana wasu daga cikin kyawawan halayen mahaifinta da ba kowa ke sani ba.

Source: Twitter
Ta ce:
“Lokacin da ya ke jinya, na je Landan na duba shi. Bayan ya ji sauƙi, na ce masa zan koma Najeriya. Sai ya ce min, ‘Ina za ki je? Na ce masa zan koma Najeriya, sai ya ce, ‘To, gaishe min da ‘yan Najeriya.’”
“Shi mutum ne mai haƙuri da juriya. Mahaifi na ba ya son hayaniya. Ba za ka zage shi ya rama ba, sai dai kawai ya rika kallon ka.”
Dalilin wasu ma yafe wa Buhari
Ibrahim Aminu da Khalil Ibrahim sun gana da Legit, inda suka bayyana cewa sun yi mamakin yadda jama'a suka riƙa yafe wa tsohon shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan
An fara fito da bayanai kan 'cabal', Gambari ya fallasa yadda aka mamaye gwamnatin Buhari
Sai dai sun ce ba haka kawai jama'a ke yafe wa ba, sun lura Buhari mutumin kirki ne a matsayinsa na ɗan adam.
Ibrahim ya ce:
Shi Buhari a kan kansa ba za a ce masa ya saci kuɗin jama'a ba, sai dai a zarge shi da sakaci ya bari an yi sata. Ina jin shi yasa jama'a ke yafe masa. Ni ma na yafe."
A kalam Khalil:
Ba daɗi ana ta zavin mutum, duk sai ya ba ni tausayi. Amma na ji mutane da yawa sun ce sun yafe masa. Allah Ya gafarta masa."
'Ya ba ni dama,' Tsohon hadimin Buhari
A baya, kun ji Bayo Omoboriowo, tsohon mai ɗaukar hoto ga marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana yadda ya shafe shekaru takwas yana aiki da shi.
Tsohon mai ɗaukar hoton shugaban ya nuna alhini bisa rasuwar Buhari tare da bayyana yadda tsohon shugaban ya taka rawa wajen ciyar da aikinsa gaba har ya kai matsayin da yake.
Ya ce shekaru da ya shafe yana aiki da Buhari sun kasance masu albarka, saboda ya samu cikakken goyon baya da yarda daga shugaban ba tare da ya rika hana shi abin da ya dace ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng