'Bai Mutunta Kakana ba': Jikan Shehu Shagari bai Ji Dadin Abin da Buhari Ya Yi a 2018 ba
- Jikan marigayi tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari ya yabawa Bola Tinubu kan karrama Muhammadu Buhari bayan rasuwarsa
- Nura Muhammad Mahe ya ce Buhari bai halarci jana’izar Shagari ba a 2018, kuma bai amince da jana'izar gwamnati ba lokacin da yake mulki
- Ya ce rashin girmama Shagari ya nuna sabanin siyasa da ke tsakaninsu, amma ya nemi a koyi darasi daga halin Tinubu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Jikan tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari ya kwarara yabo ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Nura Muhammad Mahe ya yaba wa Bola Tinubu ne bisa girmama marigayi Muhammadu Buhari da jana'iza ta kasa.

Source: Twitter
Buhari: An yabawa kokarin Bola Tinubu
A wata sanarwa da ya fitar daga Sokoto a Laraba, Mahe ya ce halartar Tinubu da kafa kwamitin jana’iza ya nuna kima ga shugabanni, cewar Punch.

Kara karanta wannan
UNIMAID: An faɗi babban dalilin da ya sa Tinubu ya sauya sunan jami'a saboda Buhari
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wannan mataki ya nuna jagoranci na gaskiya da hadin kan kasa, duk da cewa Buhari bai yi wa Shagari irin wannan ba.
A cewarsa:
“Wannan ya bambanta da yadda kakana, Shehu Shagari, ya fuskanta a lokacin gwamnatin Buhari."
Buhari bai halarci jana'izar Shagari ba
Ya tuna cewa lokacin mutuwar Shagari a 2018, Buhari bai halarci jana’izar ba, kuma bai amince da jana’izar gwamnati ba.
Shagari ya rasu ne ranar 28 ga Disamba, 2018, aka binne shi ranar 29, amma Buhari bai je ba duk da yana cikin kasar.
Sai dai Buhari ya kai ziyara ta jaje zuwa Sokoto, inda ya rattaba hannu a kundin ta’aziyya bayan mutuwar tsohon shugaban.
A ranar 31 ga Disamba, 1983 ne Buhari ya kifar da gwamnatin Shagari ta hanyar juyin mulki lokacin yana soja.
Mahe ya ce maimakon Buhari ya halarta, sai ya tura Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, domin wakiltar gwamnati.
“Wannan abin ciwo ne ga dangin Shagari da 'yan Najeriya da suka sa rai domin girmama shugaban farko na mulkin farar hula.”
- Cewar Mahe

Source: Twitter
Buhari: An bukaci yin koyi da halayen Tinubu
Ya bayyana cewa watsi da Shagari ya nuna sabanin siyasa da bai warware ba har zuwa mutuwa, yana mai bayyana bakin cikinsa.
Duk da haka, Mahe ya ce kamata ya yi a koyi da Bola Tinubu, inda ya ce girmama shugabanni ya kamata ya wuce bambancin siyasa.
Ya kammala da addu’a ga dukkan shugabannin da suka rasu, yana mai cewa tarihinsu wani muhimmin bangare ne na tarihin Najeriya, Vanguard ta ruwaito.
Yunkurin jin ta bakin wasu daga cikin jami’an gwamnatin Buhari bai yi nasara ba, domin da dama sun ce har yanzu suna makoki.
Yusuf Buhari ya yi godiya ga Tinubu
Kun ji cewa 'dan tsohon shugaban kasa ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa mutunta mahaifinsa, Muhammadu Buhari da jana’iza ta kasa da aka shirya.
Yusuf Buhari ya yaba da goyon bayan gwamnati, Majalisa, gwamnoni da 'yan Najeriya da suka jajanta musu tare da halartar jana’izar da aka yi.
Ya fadi hakan yayin taron majalisar zartarwa na musamman da aka shirya saboda marigayin a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng
