Hakeem Baba: Dattijon Arewa Ya Tsage Gaskiya kan 'Kurakuran' Buhari
- Dattijon Arewa, Hakeem Baba-Ahmed ya ce Muhammadu Buhari mutum ne mai niyya mai kyau amma bai samu damar aiwatar da su ba
- Tsohon hadimi a fadar shugaban kasan ya ce talaka ya nemi ceto a wurin Buhari, amma wahala ta ci gaba da dabaibaye rayuwarsa
- Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana yadda rashawa da salon mulki suka hana shugaba Muhammadu Buhari samun nasara a mulkinsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon kakakin ƙungiyar dattawan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana yadda ya ke kallon rayuwa da mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Hakeem ya fara da cewa zai tuna Buhari a matsayin mutum mai niyya mai kyau, sai dai kuma Allah bai ba shi damar cika burin shi ba.

Source: UGC
Ya bayyana hakan ne a wani bidoyo BBC Hausa ta wallafa a X, inda yi yi bitar tasirin mulkin Buhari da darasin da 'yan Najeriya za su iya koya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, akwai abin da Buhari ke so ya cimma amma abubuwa sun sha bamban da fatar da ake da ita a kansa.
Ya jaddada cewa abubuwan da suka faru a lokacin mulkin Buhari su ne za su bayyana shi a tarihi, duk da cewa mutane da dama na nuna fushinsu ko goyon baya a kan irin salon mulkinsa.
Yadda talaka ya nemi ceto a wurin Buhari
A cewar Hakeem Baba-Ahmed, talakan Najeriya ya nemi mafita daga Buhari saboda ya yarda da cewa tsohon shugaban mutum ne mai gaskiya da rikon amana.
Ya bayyana cewa a 2015 talaka ya mika kuri’arsa gare shi da fatan zai kare shi daga wahala da cin hanci.
Hakeem Baba ya ce a lokacin da ya ce zai tsabtace gwamnati, sun mara masa baya amma daga baya suka fahimci cewa lamarin ba mai yiwuwa ba ne.
Ya ce a lokacin da Buhari ya nemi tazarce, sun fito fili suka yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji sake zaben shi domin kauce wa kara fadawa cikin wahala, amma mutane suka sake zabensa.
Tallafin mai da cin hanci a gwamnatin Buhari
Hakeem ya ce tallafin man fetur ya kasance wata kafa ta almundahana da cin hanci a lokacin mulkin Buhari.
Ya bayyana cewa duk da cewa Buhari ya san akwai rashawa a tsarin tallafin mai, bai iya daukar matakin da ya dace ba.

Source: Twitter
Ya kwatanta lamarin da “kadangaren bakin tulu”, yana nuni da cewa Buhari ya kasa cire tallafin mai saboda yiwuwar tashin farashin fetur.
A cewarsa, ko da ba a fadi laifin Buhari yanzu ba, tarihi ba zai manta ba, kuma suna magana ne domin shugabanni su dauki darasi.
Me ya kawo wa Buhari cikas a mulki?
A cewar Hakeem, daya daga cikin matsalar Buhari ita ce yadda bai bibiyi mukarrabansa ba bayan ya nada su.
Ya bayyana cewa Buhari ya fi yin amanna da mutumin da ya nada fiye da sa ido a kan abin da mutum ke yi.
Rayuwar da Buhari ya yi da iyalan shi
A wani rahoton, kun ji cewa wasu daga cikin 'ya'yan shugaba Muhammadu Buhari sun fadi yadda suka rayu da shi.
Hanan Buhari ta bayyana cewa marigayin mutum ne mai yawan barkwanci da kuma son zumunci.
Wata jikar marigayin ta bayyana cewa Buhari ya kula da su sosai tare da ba su kyautar dabbobi cikin wadanda ya ke kiwo.
Asali: Legit.ng

