Matatar Dangote Ta Bankado Yadda Dillalanta ke Karkatar da Fetur, Ana Sayar wa da Tsada

Matatar Dangote Ta Bankado Yadda Dillalanta ke Karkatar da Fetur, Ana Sayar wa da Tsada

  • Matatar Dangote ta gano yadda wasu dillalanta ke karkatar da fetur da aka ware don sayarwa a farashi mai rangwame
  • A baya, matatar ta samar da tsarin sayar da man fetur da dauke wa abokan hulɗarta kuɗin dakon fetur don sayar wa da sauƙi
  • Amma ta gano babbar matsala, inda waɗanda matatar ta aminta da su ke sayar da fetur da suka samu ga wasu yan kasuwa na daban

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Matatar Dangote ya bayyana takaici a kan yadda wasu daga cikin abokan hulɗarta suka karya yarjejeniyar saukaka wa talakawa.

Binciken da matatar ta gudanar ya gano wasu daga cikin abokan hulɗar na karkatar da kayayyakin zuwa ga dillalan da ba su da rajista na ana saya wa jama'a da tsada.

Kara karanta wannan

Jagoran yan ta'adda ya shiga hannu, ya fara ambato abokan hulɗarsa bayan ya ji matsa

Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote
Matatar Dangote ta fusata Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa binciken ya gano yadda wasu masu dillanci da aka ba su fetur a farashi mai rangwame domin sauƙaƙa wa jama'a na sayar wa waɗansu yan kasuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan kasuwa sun fusata matatar Dangote

Lagos Television ta wallafa cewa wannan ya karya tsarin da aka shimfiɗa domin tallafa wa abokan kasuwancinta da kuma tabbatar da wadatar fetur a faɗin ƙasa.

Dangote ya ce waɗannan dillalan na amfani da takardar rajistarsu don karɓar fetur daga matatar, amma sai su bai wa wasu masu shigo da kaya damar karɓa a madadin su.

Matatar Dangote da ke Legas
Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur da sauki Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Ya ce su kuma wadancan yan kasuwa suna sayar da shi a kasuwa a farashi mafi tsada, suna kauce wa caji na dakon mai da sauran tsarabe-tsaraben da ya hau wuyansu.

Matakin matatar Dangote kan yan kasuwa

Wannan rufa-rufa da matatar Dangote ta gano ya sa ta ɗauki matakin dakatar da tsarin sayar da man fetur a farashi mai rahusa ga abokan hulɗarsa,

Kara karanta wannan

Kalaman Buhari 3 da har yanzu suke tayar da jijiyoyin wuya duk da Allah ya masa rasuwa

Wannan na kunshe a cikin wasikar dakatarwar da aka tura ga abokan hulɗar matatar a ranar 13 ga Yuli 2025, kuma Fatima Dangote, Daraktar Ayyuka na kasuwanci ta rattaba wa hannu.

Ta ce:

“A ƙoƙarinmu na tabbatar da wadatar kayayyakin man fetur ga abokan ciniki, mun bullo da tsarin rangwame domin su samu riba mai ɗorewa."
"Amma mun samu korafe-korafe masu yawa game da sayar da kaya a farashi mai tsafa, wanda hakan ke barazana ga dorewar ayyukanmu.”

Matatar ta ce ce duk da haka, za a ci gaba da dakon kaya zuwa ga duk wanda ya riga ya biya kuɗi kafin ranar dakatarwar.

Dangote zai gina tashar jirgin ruwa

A baya, mun wallafa cewa Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya fara shirin gina tashar jiragen ruwa mafi girma a Najeriya, wanda za a gina a jihar Ogun.

A cewar Dangote, an riga an mika takardun neman izini tun watan da ya gabata domin fara aikin wannan babban aiki da ake sa ran zai taimaka wa kasuwanci.

Ya ce kyakkyawar hulɗa da Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, da irin sauƙin da ake samu daga hukumomi wajen karɓar masu zuba jari ne suka ba shi kwarin gwiwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng