NELFund: Gwamnatin Tinubu za Ta Bude Dandalin Taimakawa Dalibai Samun Aiki
- Shirin lamunin karatu na NELFund zai ƙaddamar da dandali na musamman don tallafa wa dalibai wajen samun aikin yi
- Shugaban NELFund ya ce biyan bashin zai fara ne da zarar dalibi ya samu aiki bayan kammala hidimar kasa ta NYSC
- An fara bincike kan wasu makarantu da suka ki mayar da kudin da dalibai suka biya kafin NELFUND ya biya kudin karatunsu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shirin bayar da lamunin karatu na NELFund ya bayyana cewa yana ƙoƙarin ƙaddamar da dandalin neman aiki ga daliban da suka ci gajiyar shirin.
Shugaban hukumar, Akintunde Sawyerr, ne ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja domin tunawa da shekara guda da fara shirin.

Source: Twitter
Legit ta tattaro wasu daga cikin bayanan da Akintunde Sawyerr ya yi ne a cikin wani sako da hadimin Bola Tinubu, Dada Olusegun ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ko da yake shirin bai bayar da tabbacin samun aiki kai tsaye ba, dandalin zai bai wa dalibai damar samun bayanai na ainihi kan guraben ayyuka a gida da ƙetare.
Biyan bashin NELFund zai fara bayan aiki
Sawyerr ya bayyana cewa hukumar ba za ta bar dalibai da bashi kawai ba, sai dai za ta tallafa musu har su samu kwanciyar hankali ta hanyar gina tattali.
Ya ce biyan bashin zai fara ne bayan kammala hidimar kasa ta NYSC, kuma idan ba a samu aiki ba, ba za a fara biyan bashin ba.
Rahoton VON ya nuna cewa shugaban NELFund ya ce:
“Idan ba ka da aiki, ba za ka biya ba. Amma da zarar ka samu aiki, za a cire kashi 10 na albashinka a duk wata kai tsaye.”
Ya ƙara da cewa idan dalibi ya rasa aiki ko ya ajiye, cire kuɗin zai tsaya, kuma idan ya rasu, za a goge bashin gaba ɗaya.

Source: Facebook
Makarantu sun ki mayar da kuɗin dalibai
A wani bangare na jawabin, shugaban ya yi kira ga makarantun da suka karɓi kuɗi daga dalibai kafin a biya su ta hanyar NELFund da su mayar musu da kuɗinsu.
Ya bayyana cewa hukumar ta samu korafe-korafe daga dalibai da dama da suka biya kuɗi, daga bisani kuma suka gano cewa NELFund ta riga ta biya kudin.
A cewar shi:
“Makarantu suna da alhakin mayar da kuɗin da suka karɓa ba bisa ka’ida ba. Abin takaici ne cewa wasu sun ki yin hakan,”
Ya bayyana cewa hukumomin ICPC da EFCC sun fara binciken wasu makarantu da ke kin mayar da kuɗin dalibai.
“Idan makaranta ba za ta iya mayar da kuɗin kai tsaye ga ɗalibi ba, su mayar mana, mu tabbatar ya isa hannun wanda ya dace.”
Za a bude shafin neman aiki a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da sabuwar ranar bude shafin daukar ma'aikata a hukumomi hudu.
Rahotanni sun nuna cewa an fitar da sanarwar ne bayan shafe kwanaki da fara tura bayanan masu neman aiki.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce za ta kammala gyara a shafin da kuma bude shi a ranar Litinin, 21 ga watan Yuli.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


