Kalamai Masu Ratsa Zuciya da Buhari Ya Faɗawa Tajudeen Abbas bayan Ya Zama Shugaba
- Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya tuna nasihar da marigayi Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya masa a Birtaniya
- Tajudeen Abbas ya ce bayan ya zama kakakin Majalisa a 2023, shawarar da Buhari ya ba shi ita ce ya yi shugabanci kamar bawan al'umma
- Ya ce ba zai taɓa mantawa da Shugaba Buhari ba, saboda yadda ya kasance mutum mai gaskiya da rikon addininsa na Musulunci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Abbas Tajudeen, ya bayyana nasihar da marigayi tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya masa.
Hon. Abbas Tajudden ya ce ya haɗu da Buhari a Birtaniya bayan ya zama kakakin Majalisar wakilai, kuma ya masa nasiha yar gajera amma mai matuƙar amfani.

Source: Facebook
Kakakin Majalisar ya faɗi haka ne a wurin taron Majalisar Zartarwa (FEC) na musamman da aka shirya domin karrama Buhari, wanda ya wallafa a shafinsa X.
Hon. Tajudeen ya tuna cewa a 2011 aka fara zaɓensa a matsayin ɗan Majalisar wakilai a Mazabar Tarayya ta Zariya a ƙarƙashin jam’iyyar CPC wacce Buhari ne ya kafa.
Tajudeen ya tuna alaƙarsa da Buhari tun a CPC
Ya bayyana cewa bayan sake zaɓensa karo na huɗu da zamansa Shugaban Majalisar Wakilai a ranar 13 ga Yuni, 2023, marigayi Buhari ya ba shi wata muhimmiyar shawara.
Tajudeen ya ce:
“Shugaba Buhari ba wani mutum ne gama gari ba a tarihin siyasar ƙasarmu. Ya kasance mutum mai natsuwa, mai ɗabi’a da nagarta, da kuma cikakken hangen nesa.
"A wani lokaci da mutane suka fi karkata ga son duniya, shi ya zaɓi rayuwa mai sauƙi mai cike da hidima ta gaskiya. Ya kasance mai kaunar iyalinsa kuma mai riko da addinin Musulunci.
"Daga cikin halayensa akwai barkwanci da ƙasƙantar da kai, duk da tsaurin da yake da shi a fagen aiki. Buhari ya yi imani da cewa rayuwa ƙalilan ce, kuma akwai sakamako a Lahira.

Kara karanta wannan
"Kamar ya sani," Kalaman da Buhari ya faɗa game da mutuwarsa kafin ya sauka daga mulki
Wane taimako Buhari ya yiwa Tajudeen?
Tajudeen ya ci gaba da cewa ya ɗauki Buhari a matsayin shugaba, abokin shawara, jagora wanda ya taimaka masa wajen tafiyar da harkokin jama'a yadda ya dace.
"Tafiyata ta siyasa ta fara ne tun a 2011 a ƙarƙashin tutar CPC, jam’iyyar da aka kafa bisa nagartarsa da halayyarsa.
“’Yan shekaru bayan na zama ɗan Majalisa, ya zo ya kaddamar da wasu daga cikin ayyukan mazabata, ni ne mamba na farko daga Majalisar Wakilai a ƙarƙashin CPC da ya samu irin wannan girmamawa."

Source: Twitter
Kalaman da Buhari ya faɗawa Tajudeen Abbas
Dangane da nasihar da ya masa bayan ya zama kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen ya ce Buhari ya shawarce shi da ya zama bawan al'umma.
Ya ƙara da cewa:
“A baya-bayan nan a 2023, a wata ganawa da muka yi a ƙasar Birtaniya bayan na zama Shugaban Majalisa, ya tarbe ni da farin ciki.
"Shawararsa ta kasance yar kaɗan mai ma'ana, ya ce mani, 'ka yi shugabanci tamkar bawa, ba a matsayin uban gida ba', maganar ƴar kaɗan amma ta shige ni ta zama madubi a rayuwata."
Tinubu ya sanya wa UNIMAID sunan Buhari
A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya canza sunan jami'ar Maiduguri zuwa 'Jami'ar Muhammadu Buhari' domin karrama marigayin.
Shugaba Tinubu ya ce rayuwar Buhari cike take da kamun kai, gujewa amfani da iko da abin duniya, da tsayawa kan gaskiya komai ɗacinta.
Ya bayyana haka ne a taron FEC na musamman da aka shirya domin karrama tsohon shugaban ƙasar, wanda Allah ya yiwa rasuwa a Landan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

