Bayan Buhari, Bola Tinubu Zai Je Jihar Kano Ta'aziyyar Aminu Dantata
- Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja yau domin kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnatin Kano da iyalan marigayi Alhaji Aminu Dantata
- Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya bayyana ziyarar a matsayin alamar haɗin kan ƙasa da girmamawa ga dattawan Arewa
- An riga an kammala shirye-shiryen tsaro da sufuri don tabbatar da ziyarar ta gudana cikin lumana ba tare da tashin hankali ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar ta’aziyya a jihar Kano yau Juma’a, 18 ga Yuli, domin jaje ga gwamnatin jihar da kuma iyalan marigayi Alhaji Aminu Alasan Dantata.
Alhaji Dantata, ɗan kasuwa kuma mai taimako da jinkan marasa shi, ya rasu ne a Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a ranar 28 ga Yuni 2025, yana da shekara 94 a duniya.

Source: Twitter
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da labarin ziyarar a wani sako da ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa an birne marigayin makabartar Baqi'a da ke birnin Madina mai tsarki a Saudiyya a ranar 1 ga Yuli, 2025.
Tinubu bai je jana'izar Dantata ba
A lokacin rasuwar Alhaji Dantata, Shugaba Tinubu yana wajen ƙasar, amma ya aika da wasu ministocinsa domin su wakilce shi a jana’izar da aka yi a Saudiyya.
Ministan tsaro ne ya jagoranci tawagar ministocin da suka halarci jana’izar a madadin shugaban ƙasa, a matsayin girmamawa ga marigayin mai shekaru 94.
Abba ya yaba da ziyarar Tinubu a Kano
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa wannan ziyarar da Shugaba Tinubu ke shirin kaiwa alama ce ta haɗin kan ƙasa da girmamawa ga mutanen Kano.
Ya ƙara da cewa Dantata ya bar gadon sadaukarwa, kyauta da kuma inganta tattali, wanda ya shafi rayuwar dubban mutane a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan
Hoton yadda Aisha Buhari ta rungume tutar da aka lulluɓo gawar mijinta ya ja hankali
Kira ga al’umma su tarbi Bola Tinubu
Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga al’ummar Kano da su tarbi Shugaba Tinubu cikin mutunci da kima, kamar yadda al’adun jihar ke koyarwa na karɓar baƙi da girmama shugabanni.
Sanusi Bature ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya ce:
“A wannan lokaci na jimami da tunawa da marigayin dattijon, ya kamata mu tarbi shugaban ƙasa cikin tsari da natsuwa,”

Source: Twitter
An gama shirye-shiryen tsaro a Kano
Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa an tanadi tsare-tsare na tsaro da sauran shirye-shiryen da suka kamata don tabbatar da cewa ziyarar Tinubu ta kasance cikin nasara
Sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis ta bayyana cewa gwamnati tana aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin ganin an gudanar da ziyarar cikin aminci da kwanciyar hankali.
Malaman addini sun je ta'aziyya Daura
A wani rahoton, kun ji cewa malaman addinin Musulunci a Najeriya sun ziyarci Daura na jihar Katsina domin yi wa iyalan Muhammadu Buhari ta'aziyya.
A bangaren Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau da jama'ar shi sun ziyarci gidan Buhari kamar yadda Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi irin ziyarar.
Limamin masallacin kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari ya kai ziyara shi ma, kuma shi ya rufe taron da aka yi da addu'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

