Badakalar N110bn: Yahaya Bello Ya Yi Rashin Nasara a Kotu

Badakalar N110bn: Yahaya Bello Ya Yi Rashin Nasara a Kotu

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci kan buƙatar da Yahaya Bello ya gabatar a gabanta
  • Kotun ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan na Kogi kan ba shi fasfo ɗinsa domin zuwa Birtaniya a duba lafiyarsa
  • Hukumar EFCC ce dai ta shigar da tsohon gwamnan ƙara a gaban kotun kan badaƙalar N110.4bn

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mai shari'a Maryanne Anineh ta babbar kotun birnin tarayya Abuja da ke Maitama, 2025, ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Adoza Bello.

Mai shari'ar ta yi watsi da buƙatar Yahaya Bello ta a sako masa fasfonsa domin tafiya zuwa Birtaniya neman magani.

Kotu ta ki amincewa da bukatar Yahaya Bello
Kotu ta yi watsi da bukatar Yahaya Bello Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan ne yayin zaman kotun na ranar Alhamis, 17 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Kogi: Tsohon gwamna, Yahaya Bello ya ƙara aure a wani bidiyo, ya rufe ƙofa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da Yahaya Bello tare da Umar Shuaibu Oricha da Abdulsalami Hudu a gaban kotun kan tuhume-tuhume 16 da suka shafi cin amana da kuma halasta kudaden haram da suka kai N110.4bn.

Yahaya Bello ya miƙa buƙata gaban kotu

A zaman da ya gabata, lauyan Yahaya Bello, J.B. Daudu, SAN, ya gabatar da wata buƙata da aka rubuta a ranar 19 ga Yuni, 2025 kuma aka miƙa wa kotu a ranar 20 ga Yuni, 2025, yana roƙon a sako masa fasfonsa na ɗan wani lokaci.

Ya buƙaci a ba shi fasfon nasa ne domin ya je a duba lafiyarsa a Birtaniya, tare da alƙawarin dawo da fasfon bayan dawowarsa.

Sai dai a martaninsa, lauyan masu ƙara, Chukwudi Enebeli, SAN, ya roƙi kotu da ta yi watsi da bukatar, yana mai cewa hakan zai sauya sharuɗɗan beli da kotun ta gindaya, inda aka umurce shi da ya miƙa fasfonsa ga kotu.

Kara karanta wannan

Zambar N2.2bn: Babbar kotu ta kawo karshen shari'ar tsohon gwamnan Ekiti da EFCC

Lauyan masu ƙara ya ƙara da cewa wanda ake tuhumar ya ci mutuncin tsarin shari’a, saboda yana da irin wannan buƙata a wata kotu daban wacce bata yanke hukunci ba tukuna.

A ci gaba da sauraron ƙarar a ranar Alhamis, lauyan EFCC, Jami’u Agburo, ya shaida wa kotu cewa sun shirya domin a yanke hukunci kan buƙatar.

Wane hukunci kotun ta yanke?

A hukuncinta, mai shari’a Maryanne Anineh ta bayyana cewa kotunta ba ta da hurumin yanke hukunci a kan buƙatar, kasancewar fasfon ba ya hannunta, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Kotu ta zartar da hukunci kan bukatar Yahaya Bello
Yahaya Bello ya yi rashin nasara a gaban kotu Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Source: Facebook
"Abin da ke bayyane shi ne, fasfo ɗaya ba zai kasance a hannun kotuna biyu a lokaci daya ba. Tunda wanda ake tuhuma ya amsa da kansa cewa ya ajiye fasfon a babbar kotun tarayya, babu dalilin da zai sa wannan kotu ta bayar da wani umarni."
"Kotuna ba sa bayar da umarni da zai zama babu amfani, kuma saboda haka, wannan kotu ba za ta bayar da wani umarni da zai zama mara amfani ba."

- Mai shari'a Maryanne Anineh

Daga nan sai ta ɗage shari’ar zuwa ranakun 8 da 9 ga Oktoba, da 13 ga Nuwamba, 2025, domin cigaba da sauraron ƙarar.

Kara karanta wannan

"Bai so": Buba Galadima ya fadi dalilin jawo Buhari cikin harkar siyasa

Yahaya Bello ya ƙara aure

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya raya Sunnah bayan ya ƙara aure.

Tsohon gwamnan ya angwance da amaryarsa a birnin tarayya Abuja, wanda hakan ke nuna cewa ya rufe ƙofa.

Matarsa ta uku ta tabbatar da ƙarin auren da ya yi, inda ta yi wa amaryarsa maraba zuwa cikin iyalansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng