Ana Saura Shekara 2 Ya Sauka, Gwamna Abba Ya Fadi Aikin da Ya Rage Masa a Kano
- Mai girma Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gamsu da irin ayyukan da gwamnatinsa take aiwatarwa
- Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya cika mafi yawan alƙawuran da ya ɗauka a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe
- Gwamnan ya kuma shawarci jami'an gwamnatinsa da suka kasance masu gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da ayyukansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ta aiwatar da kaso 85% cikin 100% na alƙawuran da ta dauka wa al’ummar jihar Kano lokacin yaƙin neman zaɓe.
Gwamna Abba ya bayyana cewa sauran kaso 15% cikin 100% ne kawai ya rage yayin da ya rage masa saura shekara biyu ya kammala wa'adinsa.

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin rantsar da shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano, Dr. Sulaiman Wali Sani, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan
"An karya doka," Abin da Atiku ya yi ana jimamin rasuwar Buhari ya harzuƙa Ministan Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran waɗanɗa aka rantsar sun haɗa da darakta janar na sashen ayyuka na musamman, Manjo Janar Sani Muhammad (mai ritaya), da kuma mashawarta na musamman guda 11 a ranar Alhamis.
Gwamna Abba ya cika alƙawura a Kano
Gwamna Abba ya ce nasarar da aka samu ta biyo bayan cikakken nazari da kimanta aikin da gwamnatin ta gudanar a cikin shekaru biyu da suka wuce.
“Na ji daɗi cewa makon da ya gabata, lokacin da na duba sakamakon aikinmu da alƙawuran da muka ɗauka ga jama’a tun daga matakin rumfunan zaɓe, mun cimma kashi 85% cikin 100% cikin shekaru biyu."
"Don haka, abin da ya rage mana yanzu shi ne kaso15% cikin 100% da za mu kammala a cikin shekara biyu masu zuwa."
"Mun gabatar da wannan batu a gaban majalisar zartarwa ta jihar Kano. Muna ragowar kaso 15% kuma muna da shekaru biyu. Don haka, za mu duba matakai uku da za mu bi."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba ya ƙara da cewa gwamnati ba za ta tsaya hutu ba, domin kuwa za ta ƙaddamar da sababbin tsare-tsare da shirye-shirye da za su ƙara tasiri ga rayuwar al’ummar Kano.
“Muna shirin kawo sababbin shirye-shirye da hanyoyi waɗanda, Insha Allah, za su ci gaba da haifar da tasiri mai kyau ga rayuwar al’ummar wannan jiha. Kuma ba za mu iya yin hakan mu kaɗai ba, sai tare da goyon bayan ku duka."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Source: Twitter
Wace shawara Gwamna Abba ya ba da?
Abba ya kuma buƙaci dukkan jami’an gwamnatin da su rungumi gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da dukiyar jama’a, tare da yin kira da su rika bayar da sahihin ra’ayi da shawarwari.
“Idan akwai wata matsala, kada ku je ku yi ta surutu. Kada ku je ku fara bincike. Saboda idan kun fara bincike, kuna binciken kanku ne."
"Kada ku rika ɓoye gaskiya, ku zo kai tsaye ku gaya mana inda muke daidai da inda muke kuskure. Wannan shi ne dalilin da yasa kuke a wajen. Ku tabbatar da gaskiya da rikon amana a aikinku."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Abba za ta buɗe makarantu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano, ta ware maƙudan kuɗade don gyara makarantun kwana.
Gwamna Abba ya amince da kashe N3.3bn domin yin gyara da sabunta makarantun kwana 13 na jihar.
Matakin na Gwamna Abba na zuwa ne dai bayan an kulle makarantun a lokacin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

