Abin da Sarki Sanusi II Ya Yi a Fadarsa domin Karrama Marigayi Buhari
- Rashin ganin Muhammadu Sanusi II a jana'izar Muhammadu Buhari a Daura ya jawo ce-ce-ku-ce, duk da halartar Aminu Ado Bayero a wurin jana'izar
- Masarautar Kano ta fitar da sanarwa inda aka saukar da tuta a fadar Sanusi II domin nuna alhini kan rasuwar tsohon shugaban kasa
- Wani makusancin Sarki Sanusi II ya bayyana cewa Mai marrtaban yana London lokacin jana'izar, shi yasa bai samu halarta ba duk da fadar ta tura ta'aziyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wasu mutane sun yi ta maganganu bayan rashin ganin Sarki Muhammadu Sanusi II a jana'izar Muhammadu Buhari.
An gudanar da jana'izar a garin Daura a ranar Talata 15 ga watan Yulin 2025 inda Bola Tinubu da manyan Najeriya suka halarta.

Source: Facebook
Wani bidiyo da Masarautar Kano ta wallafa X ya nuna yadda fadar Sarki Sanusi II ta saukar da tuta domin nuna alhini game da rasuwar Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari: Maganganu kan rashin ganin Sanusi a Daura
Hakan ya biyo bayan maganganu da ake ta yi kan rashin ganin basaraken a wurin jana'izar wanda aka fitar da sanarwa kan haka.
Wani makusancin Sarkin da ake kira Muhammadu Dallatu ya bayyana musabbabin rashin samun damar halartar jana'izar da basaraken ya yi zuwa Daura.
A cikin sanarwar, ya ce Sarki Sanusi II ya kasance a birnin London da ke kasar Birtaniya shi yasa bai samu damar dawowa Najeriya ba.

Source: Twitter
Rasuwar Buhari: Ziyarar Aminu Ado zuwa Daura
Tun farko, an gano Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero a Daura inda ya halarci jana'izar Buhari wanda ya kara jawo maganganu.
Aminu Ado ya dura a Daura ne da safiyar ranar Talata 15 ga watan Yulin 2025 domin shaida ganin karshe ga tsohon shugaban kasa.
Zuwan Aminu Ado garin Daura saboda jana'iar Buhari ya jawo gori ga bangaren Sanusi II cewa bai halarci jana'izar ba.

Kara karanta wannan
'Abin da ya sa Sarki Sanusi II bai halarci jana'izar Buhari ba da aka yi a Daura'
Wasu da ake zaton masoyan Aminu Ado ne suka ce ai daman idan Sarki na gaskiya yana taro ba a ganin na bogi a wurin.
Rasuwar Buhari: Abin da Sanusi II ya yi
Sai dai daga bisani, fadar Sanusi II ta nuna alhini kan rasuwar bayan tura sakon ta'aziyya tun ranar mutuwar Buhari.
A cikin wani bidiyo, an gano yadda aka yi kasa-kasa da tuta da ke saman fadar domin nuna jimami saboda rasuwar Buhari.
Sanarwar ta ce:
"Mai Martaba, Sarkin Kano, Khalifah Dr. Muhammad Sanusi II, CON ya umarci yin kasa da tuta domin nuna alhini kan rasuwar Muhammadu Buhari."
Matar Sarki Sanusi I ta rasu a Kano
Kun ji cewa Masarautar Kano ta shiga jimami bayan rasuwar iyalin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, Yaya Jide da 'yarsa, Goggo Ummahani.
Majiyoyinmu sun tabbatar da cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ne ya jagoranci sallar jana’izar matan biyu a ranar Laraba, 16 ga Yulin 2025
Wannan babban rashi a masarauar Kano na zuwa ne yayin da ake cikin jimamin rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya rasu a London.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
