Dalibai Sun Hallaka Abokan Karatunsu 2 a Kano, Gwamnati Ta Shiga Maganar

Dalibai Sun Hallaka Abokan Karatunsu 2 a Kano, Gwamnati Ta Shiga Maganar

  • Gwamnatin Kano ta fusata bayan samun labarin yadda wasu dalibai suka hallaka abokan karatunsu a makarantar kwana a jihar
  • Tuni aka bada umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan kisan dalibai biyu a makarantar sakandare ta gwamnati da ke Bichi
  • Kwamishinan ilimi na Kano, Dr. Ali Makoda ya yiwa iyalan yaran biyu da aka kashe alkawarin tabbatar da gaskiya da adalci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Dr. Ali Makoda, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan mutuwar wasu dalibai guda biyu.

Ana zargin daliban makarantar da kashe yan uwansu dalibai guda biyu bisa zargin aikata wani laifi a makarantar kwana ta Bichi.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano ta fusata kan kisan dalibai Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan na cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kai na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Balarabe Kiru, ya fitar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Za a yi wa shugaba Buhari addu'a a coci ranar Lahadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin an kashe Hamza Tofawa da Umar Dungurawa, bayan yan uwansu dalibai sun kai masu hari da ƙarafa da suka samu a cikin makarantar.

Gwamnatin Kano ta tabbatar da kisan dalibai

A wata tattaunawa da Legit ta wayar tarho, Balarabe Abdullahi Kiru ya tabbatar da kisan, inda ya ce gwamnati za ta tabbatar da gaskiya da adalci.

Ya bayyana cewa:

“Kwamishinan ilimi ya tabbatar wa da al’umma cewa za a gudanar da bincike na gaskiya da adalci domin gano musabbabin lamarin.”
An kashe dalibai 2 a Kano
Gwamnati ta fara binciken kisan dalibai a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Kwamishinan, ta bakin babban sakataren na ma’aikatar, Bashir Muhammad, ya ce za a tabbatar da adalci ga dukkanin bangarorin da abin ya shafa.

Ya ce:

"Wannan mummunan lamari ya biyo bayan wani hukunci da wasu manyan dalibai suka ɗauka, inda suka yanke shawarar hukunta waɗanda suka mutu bisa zargin aikata wani laifi.”

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi dalibai

Babban Sakataren wanda ya kai ziyara makarantar, ya gargadi dalibai da su kasance masu lura da kai da kuma guje wa ɗaukar doka a hannunsu.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta buɗe makarantu 13 da Ganduje ya rufe, za a kashe sama da N3bn a Kano

Ya ce:

“Ya kamata ku guji ɗaukar doka a hannunku, maimakon haka ku rika sanar da hukumar makaranta duk wani abu domin daukar matakin da ya dace.”

Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki kan wannan babban rashi.

Ya ce:

“A madadin gwamnatin jihar Kano, ma’aikatar ilimi da daukacin al’ummar jihar, muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan mamatan, tare da addu’ar Allah ya ba su Jannatul Firdaus.”

A nasa bangaren, daraktan makarantun sakandare na jihar, Abbas Abdullahi, ya bayyana bakin cikinsa kan lamarin.

Ya ce:

"Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin cewa za ta tabbatar da an binciko gaskiya dangane da wannan mummunan al’amari.”

An yi babban rashi a jihar Kano

A baya, mun wallafa cewa Masarautar Kano na cikin alhini bayan rasuwar wasu daga cikin iyalan marigayi Sarkin Kano na farko, Muhammadu Sanusi I, wato Goggo Ummahani da Yaya Jidde.

Kara karanta wannan

Dangote ya kinkimo babban aiki, zai gina tashar ruwa mafi girma a Najeriya

Marigayiyar Goggo Ummahani ɗiya ce ga Sarkin Kano Sanusi I, wanda ya mulki jihar daga shekarar 1954 zuwa 1963, ita kuma Yaya Jidde matarsa ce.

Duk da ba a fadi dalilin rasuwarsu ba, Mai martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, ne ya jagoranci sallar jana’izar matan biyu da safiyar Laraba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng