Mutuwar Buhari: Faɗa Ya Kaure tsakanin Adesina da Likitoci kan Ingancin Lafiya a Najeriya

Mutuwar Buhari: Faɗa Ya Kaure tsakanin Adesina da Likitoci kan Ingancin Lafiya a Najeriya

  • Likitoci sun karyata kalaman Femi Adesina da ya yi kan rashin lafiyar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
  • Femi Adesina ya ce Buhari zai mutu da wuri da ace ya dogara da asibitocin Najeriya kawai lokacin jinyarsa
  • Farfesoshi da manyan likitoci sun ce akwai ƙwararrun likitoci a Najeriya, kuma da dama daga cikinsu suna aiki a asibitocin ketare

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Ana cigaba da ce-ce-ku-ce kan ingancin bangaren lafiya a Najeriya bayan rasuwar Muhammadu Buhari.

Likitoci sun karyata ikirarin tsohon mai magana da yawunsa, Femi Adesina cewa Buhari zai mutu da wuri da a ce ya dogara da asibitocin Najeriya.

An soki hadimin Buhari kan ingancin lafiya a Najeriya
An kaure da fada tsakanin hadimin Buhari da likitoci kan ingancin lafiya a Najeriya. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Masana suka bayyana kalaman nasa a matsayin na rashin adalci ga ƙwararrun likitoci da ke ba da nagartaccen kulawa a Najeriya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An fadawa Tinubu abu 1 da Najeriya ke bukata bayan mutuwar Buhari a London

Abin da Adesina ya ce kan kiwon lafiya

A baya, Adesina ya ce Buhari ba zai yi tsawon rai ba da ace ya nemi magani a gida, inda ya kare tafiye-tafiyen neman lafiyar shugaban zuwa London.

A cewarsa:

“Buhari tun kafin zama shugaban kasa yana kula lafiyarsa a London. Don haka ba don mulki ya fara zuwa ba.
“Domin mutum ya samu damar gyara wani abu sai yana raye, yin magani a gida na iya zama barazana ga rayuwarsa.”

Mutuwar Buhari: An soki Adesina kan kalamansa

Sai dai likitoci da masana sun ce wannan batu bai nuna ainihin matsalolin tsarin kiwon lafiya da ke haddasa tafiye-tafiye ba.

Farfesa Adebayo Onajole ya ce likitoci ‘yan Najeriya ne ke yi wa ‘yan kasar aiki a waje, kuma suna da cancanta da kwarewa.

Ya ce:

“Ban amince da Femi Adesina ba, tsohon mataimakin shugaban kasa an yi masa tiyata a gida kuma yana raye har yanzu.”

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da bayyana ayyukan alheran Buhari, Malami faɗI abin da ya sani

“Wasu daga cikin likitocin da ake haduwa da su a London ‘yan Najeriya ne."
Ana ce-ce-ku-ce kan ingancin lafiya a Najeriya bayan mutuwar Buhari
Likitoci sun caccaki hadimin Buhari kan ingancin lafiya a Najeriya. Hoto: Bashir Ahmad.
Source: Twitter

Buhari: An fadi ingancin asibitoci a Najeriya

Farfesan ya ce akwai asibitoci a Najeriya da za su iya ba da kulawa irin ta kasashen waje, matsalar dai ita ce samuwar kudin jinya.

Ya ce akwai likitoci da cibiyoyi a Najeriya da za su iya ba da ingantacciyar lafiya kamar Turai ko Amurka.

Shugaban NARD, Dr. Tope Osundara, ya nuna damuwa da yadda mutuwar Buhari a Ingila ke kara rushe amincewa da asibitocin cikin gida.

Osundara ya ce hakan yana kara nuna rashin kwarin gwiwa ga tsarin lafiya da gwamnati ke jinkirta gyara.

Ya ce gwamnati ta kashe biliyoyin Naira a kan kiwon lafiya a mulkin Buhari, amma daga karshe ya mutu a asibitin kasashen waje.

“Mutuwarsa a Landan na nuni da gazawar amincewa da asibitocinmu. Hakan zai hana masu zuba jari shigowa tsarin."

- A cewar Osundara

Buhari: An shawarci Tinubu kan inganta lafiya

Mun ba ku labarin cewa dan rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya gina asibitoci da za su dace da kiwon lafiya na duniya.

Kara karanta wannan

Babbar jami'ar majalisar dinkin duniya ta yi wa Buhari shaida mai kyau

Ya ce Najeriya na bukatar asibitin zamani don dakile dogaro da kasashen waje, bayan rasuwar Muhammadu Buhari a asibitin London.

Adeyanju ya jaddada cewa aikin yana yiwuwa kafin karshen wa’adin mulkin Tinubu, idan aka nuna jajircewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.