Mai Daukar Hoton Buhari Ya Yi Bankwana da Tsohon Shugaban, Ya Fadi Halayyarsa Ta Aiki
- Bayo Omoboriowo, tsohon mai ɗaukar hoton marigayi Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ya yi aiki da tsohon shugaban
- Ya ce tun da ya samu labarin rasuwar tsohon shugaban ƙasa ya gaggauta tafiya Landan domin ɗaukar hoton Buhari na ƙarshe
- Omoboriowo, ya bayyana yadda ya gudanar da aiki na tsaron shekaru takwas na tare da Buhari ya yi masa linzami ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Bayo Omoboriowo, tsohon mai daukar hoto na musamman ga marigayi Muhammadu Buhari, , ya yi bayanin yadda ya yi aikin shekaru takwas da tsohon shugaban.
A cikin wata gajerar wasika mai ratsa zuciya, ya bayyana irin yadda tsohon shugaban kasa ya ba shi cikakken goyon baya da dama har ya kai matakin da yake a yau.

Kara karanta wannan
"An karya doka," Abin da Atiku ya yi ana jimamin rasuwar Buhari ya harzuƙa Ministan Tinubu

Source: Twitter
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Omoboriowo ya ce shekaru takwas da ya shafe yana aiki tare da Buhari ba tare da tsangwama ko katsalandan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayo Omoboriowo: "Yadda na yi aiki da Buhari"
Omoboriowo ya nanata cewa ko sau daya, tsohon shugaba, Muhammadu Buhari bai taɓa tsoma baki a cikin aikin sa ko ya hana shi yin abin da ya dace.
Ya ce:
“Na shafe shekaru takwas ina aiki a matsayin mai ɗaukar hoto na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari. A cikin wadannan shekarun, bai taɓa tsoma baki a aikina ba — ko sau daya. Ya yarda da ni matuƙa, kuma ya ba ni damar yin abin da ya dace."

Source: Twitter
Omoboriowo ya kara da cewa Buhari ya ba shi dama ya samu ci gaba a sana’ar sa, tare da bashi cikakken ikon bayyana kansa ta hanyar daukar hoto da labarta tarihin Najeriya.

Kara karanta wannan
Farfesa Pantami ya tuna kyaututtuka 2 da Buhari ya yi masa da ba zai taɓa mantawa ba
A kalamansa:
“Ya ba ni sarari in bunkasa. Ya bar ni, matashin ɗan Najeriya, in bayyana kaina ta hanyar kyamara. Ya bar ni in bada labarin Najeriya cikin gaskiya. A hakan, ya taimaka mani in nuna yadda abubuwa ke yiwuwa idan matasa suka samu dama.”
'Rasuwar Buhari ta taɓa ni', inji Omoboriowo
Mai daukar hoton, wanda ya kasance daya daga cikin masu adana tarihin gwamnatin Buhari ta fuskar hoto, ya ce da samun labarin rasuwar Buhari ya tafi Landan.
Ya ce:
“Da ya rasu, na san dole in je. Na tashi zuwa Landan don daukar hotunan karshe na rayuwarsa — ba kawai a matsayin mai daukar hoto ba, amma a matsayin wanda rayuwarsa ta sha canna saboda irin tasirinsa.Wannan tarihi ne. Wannan girmamawa ce."
“Na gode, Shugaba Buhari — saboda yarda da ni, saboda amana, da kuma saboda damar da ka ba ni na yi aiki da kai da girma. Ka tafi, amma ba za a manta da kai ba. Allah Ya jikanka da rahama Ya sa ka huta."
Diyar Buhari na kewar mahaifinta
A baya, mun wallafa cewa Daya daga cikin ’ya’yan marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hadiza Buhari ta bayyana yadda ya ji dacin rasuwar mahaifinta.
'Diyar da aka fi sani da Nana ta bayyana irin tarbiyyar da suka samu daga tsohon shugaban kasar, musamman ta fuskar riƙon amana da gudun abin da ba nasu ba.
Hadiza ta bada misali da wani lokaci a yarintarsu da ya daɗe yana ratsawa a zuciyarta, lokacin da mahaifinsu ya basu kuɗi su sayi littattafai , ta kashe canjin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
