Tashin Hankali a APC: Mutanen Buhari na CPC na Shirin Ficewa bayan Mutuwarsa
- Jam’iyyar APC na fuskantar barazanar ficewar magoya bayan Muhammadu Buhari na CPC bayan rasuwarsa
- Wasu manyan jiga-jigan tsohuwar CPC na shirin komawa jam’iyyar ADC domin gina wata sabuwar tafiya
- Jam’iyyar ADC ta ce rasuwar shugaba Buhari za ta ƙarfafa tsarin siyasar da ya kafa da kuma burinsa na gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja Abuja - Bayan rasuwar shugaba Muhammadu Buhari, ana cigaba da bayyana damuwa kan makomar siyasar mutanensa, musamman na tsohuwar jam’iyyar CPC.
Rikicin da ke kara bayyana tsakanin masu biyayya ga Buhari da jam’iyyar APC na nuna yiwuwar sauyin salo a siyasar Najeriya, musamman gabanin zaɓen 2027.

Asali: Twitter
Punch ta zanta da kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, inda ya bayyana cewa suna cigaba da karbar mutanen Buhari zuwa jam'iyyar adawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan abokan tafiyar Buhari sun fara komawa jam’iyyar ADC, yayin da wasu kuma suka fara nuna adawa da tazarcen Shugaba Bola Tinubu.
Ana fargabar 'yan CPC za su bar APC
Rahotanni sun ce tun bayan hawar Tinubu mulki a 2023, tasirin ‘yan CPC ya fara raguwa, inda wasu daga cikinsu suka fara bayyana rashin amincewa da salon mulkin shugaban kasar.
Nasir El-Rufai da Babachir Lawal na daga cikin wadanda ke kan gaba wajen nuna adawa da mulkin Tinubu, inda suke zargin APC da watsi da tsarin jam'iyyar.
Maganar Abdulsalami kan tasirin Buhari
Tsohon shugaban kasa a lokacin mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa akwai alamar samun sauyi a siyasar Najeriya bayan rasuwar Buhari.
A hirar da Channels TV ta yi da shi a London, Abdulsalami ya ce:
“Rasuwar Buhari za ta sauya siyasar Najeriya, kuma ina fata sauyin zai zama alheri.”

Asali: Getty Images
ADC ta ce rabuwar CPC da APC ya kusa
Mai magana da yawun jam’iyyar hadaka ta ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa za su cigaba da karbar mutanen Buhari.
A cewar shi:
“Yawancin magoya bayan Buhari suna tare da mu. Duk yankin Arewa yanzu yana tare da jam’iyyarmu.”
“Wannan shi ne burin Buhari tun yana raye — ya so mambobinsa su shiga hadaka domin ci gaba da tafiyar gaskiya.”
Abdullahi ya ce wasu jiga-jigan CPC da suka hada da Babachir Lawal, Nasir El-Rufai, Isa Pantami, Rotimi Amaechi da sauransu suna cikin manyan jagororin sabuwar hadakar jam’iyyun.
Duk da haka, wasu daga cikin tsofaffin jiga-jigan CPC kamar su Tanko Al-Makura, Ibrahim Gobir da Garba Datti na ci gaba da zama a APC kuma suna aiki domin nasarar jam’iyyar a 2027.
Atiku ya fita daga jam'iyyar PDP
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar adawa ta PDP.
Atiku Abubakar ya sanar da haka ne a cikin wata wasika da ya rubuta wa shugaban jam'iyyar PDP na mazabar shi.
Ana ganin sauya shekar za ta yi tasiri sosai a siyasar 2027, duk da cewa har yanzu bai fitar da sanarwa kan jam'iyyar da ya shiga ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng