Sarkin Zazzau na 18 da Manyan Sarakuna 8 da Suka Fi Daɗewa a kan Sarauta a Najeriya

Sarkin Zazzau na 18 da Manyan Sarakuna 8 da Suka Fi Daɗewa a kan Sarauta a Najeriya

  • Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya kwashe shekaru 45 a kan sarauta hakan ya sa ya shiga cikin sarakuna mafi daɗewa
  • Oba James Adelusi Aladesuru II da ke jihar Ekiti, shi ne Sarki mafi daɗewa a kan mulki, kuma har yanzu yana nan a raye a Igede-Ekiti
  • Legit Hausa ta zakulo maku fitattun sarakuna tara, waɗanda suka fi jimawa kan mulki da adadin shekarun da suka yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun - Sarkin Ijebuland, wanda ake kira da Awujale a jihar Ogun, Oba Sikiru Kayode Adetona, ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.

Mai martaba Sarkin ya rasu yana da shekaru 91, sa'o'i kaɗan bayan sanarwar rasuwar abokinsa na tsawon lokaci, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Sarakuna mafiya daɗewa a sarauta a Najeriyam
Manyan Sarakuna 9 mafi daɗewa a kan karagar mulki a Najeriya Hoto: Zazzau Emirate, @OgbeniDipo
Source: Twitter

Oba Adetona ya hau karagar mulki a 1960, kuma yana daga cikin sarakunan gargajiya da suka fi dade wa a kan sarauta a Najeriya, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

An fadi lokacin da ake sa ran birne Muhammadu Buhari a Daura

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana girmama shi matuka saboda gudunmawarsa wajen ci gaban siyasa da zamantakewa a Ijebuland da jihar Ogun baki ɗaya.

Jerin Sarakuna 9 mafi daɗewa kan mulki

Legit Hausa ta haɗa maku jerin sarakuna tara da suka fi dadewa a mulki a Najeriya:

1. Oba Sikiru Kayode Adetona (Awujale na Ijebuland)

Oba Sikiru Kayode Adetona ya kasance Awujale mai daraja a masarautar Ijebu. An naɗa shi sarki a ranar 2 ga Afrilu, 1960.

An haife shi a ranar 10 ga Mayu, 1934, kuma ya yi mulki na tsawon shekaru sama da 65 kafin rasuwarsa a ranar 13 ga Yuli, 2025. Ya fito ne daga gidan sarauta na Anikinaiya.

Marigayi Oba Sikiru Kayode Adetona.
Sarakuna mafi daɗewa a kan sarauta a Najeriya Hoto: @OgbeniDipo
Source: UGC

2. Oba Okunade Sijuwade

Oba Sijuwade shi ne Ooni na 50 a masarautar Ife. Ya hau karagar Sarkin Ife a 1980 kuma ya yi mulki har zuwa rasuwarsa a 2015, ma'ana ya kwashe shekaru 35 a kan sarauta.

Kara karanta wannan

Buhari: Jerin shugabannin da Najeriya ta rasa tun 'yancin kai

A rahoton The Nation, Sarkin ya taka rawar gani wajen raya al'adun Yarbawa, ɗorewar zaman lafiya, da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

3. Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III

Oba Adeyemi, tsohon Alaafin na Oyo ya yi mulki na shekaru 52 daga 18 ga Nuwamba, 1970, har zuwa mutuwarsa a ranar 22 ga Afrilu, 2022.

Shi ne Sarkin Oyo watau Alaafin da ya fi dadewa a kan karagar sarauta kamar yadda tarihi ya nuna.

4. Oba Oladunni Oyewumi Ajagungbade III

Oba Ajagungbade III ya yi mulki a matsayin Soun na Ogbomoso daga 24 ga Oktoba, 1973, zuwa 12 ga Disamba, 2021, ya yi shekaru 48 a kan sarauta.

Sarkin wanda ya rasu a watan Satumban, 2021, ya bar tarihin kawo ci gaba a garin Ogbomoso.

5. Oba Erediauwa

Oba Erediauwa ya kasance Sarki na 38 a masarautar Benin da ke Edo. Ya hau karagar mulki a ranar 23 ga Maris, 1979, inda ya yi saruta tsawon shekaru 37 zuwa 29 ga Afrilu, 2016.

An haife shi a ranar 22 ga Yuni, 1923. Kafin hawansa kan sarauta, an fi saninsa da sunan Prince Solomon Aiseokhuoba Igbinoghodua Akenzua.

Kara karanta wannan

Sun kwanta dama: Buhari, Dantata da wasu manyan ƴan Najeriya da suka rasu a 2025

6. Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris

Alhaji Shehu Idris ya kasance Sarkin Zazzau na 18. Ya hau karagar sarauta a ranar 8 ga Fabrairu, 1975, har zuwa rasuwarsa a ranar 20 ga Satumba, 2020, ya kwashe shakara 45 yana mulki.

Marigayi Alhaji Shehu Idris mutum ne da aka sanshi da kaunar zaman lafiya, nutsuwa da jajircewar wajen kawo ci gaba a yankin masarautar Zazzau.

Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.
Alhaji Shehu Idris na cikin sarakuna mafi daɗewa a sarauta Hoto: @Zazzau_Emirate
Source: Twitter

7. Dr. Jonathan Danladi Gyet Maude

Dr. Jonathan Danladi Gyet Maude shi ne Sarkin masarautar Ham (Jaba) a Kudancin jihar Kaduna.

An naɗa shi a 1974, kuma har yanzu yana mulki, shekaru sama da 51 kenan tun bayan hawansa kan sarauta.

Ya shahara da juriya da goyon bayan talakawansa, har ma yana soke bukukuwan Tuk Ham a idan jama'arsa na cikin wahala.

8. Oba James Adelusi Aladesuru II

Oba Aladesuru II shi ne Onigede na Igede-Ekiti a jihar Ekiti. Ya karɓi sarauta a ranar 26 ga Yuni, 1959, kuma har yanzu shi ne Sarki bayan shekaru 66.

Kara karanta wannan

Kalaman Buhari 12 da suka yi amo a Najeriya kuma za su sa a rika tunawa da shi

Shi ne Sarkin da ya fi dadewa a Najeriya, kuma daya daga cikin mafi dadewa a nahiyar Afirka.

Ya jagoranci harkokinci gaban ilimi, kiwon lafiya, da zamantakewa a garin Igede-Ekiti da ke jihar Ekiti.

9. Sarkin Kagoro, Gwamma Awan

Gwamna Awan ya kasance sarkin Gworog (Kagoro) a Kudancin Jihar Kaduna. An haife shi a 1915 a garin Ucyo (Fadan Kagoro).

Ya hau mulki a 1945, inda ya shafe shekaru 63 yana sarauta har zuwa rasuwarsa a ranar 1 ga Oktoba, 2008.

Olubadan na ƙasar Ibadan ya kwanta dama

A wani labarin, kun ji cewa Mai Martaba Olubadan na Ibadanland, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu bayan shafe kusan shekara guda a kan mulki.

Rasuwar Oba Olakulehin, wanda aka haifa a ranar 5 ga Yuli, 1935, ta zo ne kasa da kwana biyu bayan ya cika shekaru 90 da haihuwa.

Sarki Olakulehin, wanda ya hau karagar mulki a watan Yuli na shekarar 2024, ya rasu da safiyar Litinin, 7 ga Yuli, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262