Diyar Buhari, Hadiza Ta Fadi Tafarkin da Mahaifinsa Ya Dora Yaransa a kai
- Daya daga cikin yaran tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta bayyana yadda mahaifinsu ya yi masu tarbiyya
- Hadiza Buhari ta ce mahaifinsu ya koya masu kada su taɓa karɓar ko amfani da dukiyar da ba nasu ba ba tare da izini ba
- Hadiza ta jaddada cewa Buhari ya rayu cikin sauƙi da ƙanƙan da kai, yana guje wa tara kadarori kuma ya kasance mai tsoron Allah
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Daya daga cikin ’ya’yan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Hadiza Mohammed, ta bayyana irin tarbiyyar da suka samu daga mahaifinsu tun suna ƙanana.
Hadiza, wacce aka fi sani da Nana, ta ce Buhari ya koya mata da ’yan uwanta cewa kada su taɓa karɓar abin da ba nasu ba.

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Hadiza ta tuna wani lokaci tun suna yara, wanda ya daɗe a kwakwalwarta, dangane da darasin da mahaifinsu ya basu kan kasancewa masu hali nagari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Diyar Buhari: 'Baba ya ba mu tarbiyya'
Hadiza Mohammed ta kara da cewa mahaifinsu bai yarda su cinye hakkin wasu ba, komai kankantarsa.
Ta ce:
“Ba zan taɓa mantawa ba lokacin da muke yara, Baba ya tura mu sayen littattafan rubutu, bayan mun sayo, sai aka ba mu canji N15."
Maimakon mu dawo da kuɗin canjin wurin Baba, sai muka tsaya a wani shago muka say ealewa. Da muka koma gida, Baba ya tambaye mu ina canjin, sai muka ce mun kashe kuɗin ne.”

Source: Twitter
Ta ci gaba da cewa wannan karamin abu ne ya zama babban darasi a rayuwarsu, inda ya shaida masu cewa kada su kara cin abin da ba nasu ba.
Hadiza ta ce:
“Sai ya ce mana: ‘Kada ku ci abin da ba naku ba’, ko kuma ‘kar ku ɗauki abin da na wasu ne’. Muna godiya ga Allah da irin tarbiyyar da muka samu daga wurin Baba.”
Hadiza Buhari: ‘Babanmu ya rayu cikin sauƙin kai'
Hadiza ta bayyana cewa mahaifinta ya rayu cikin sauƙi da ƙanƙan da kai, ba tare da bin duniya da son tara kadarori ba, kuma ya kasance musulmi mai tsoron Allah har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
Ta ce:
“Rasuwar Baba abin takaici ce. Babu wata mutuwa da ba ta da ciwo ko ba ta da zafi. Amma muna godewa Allah cewa Baba ya rayu cikin sauƙin kai, irin rayuwar da wasu daga cikin Manzannin Allah suka rayu da ita.”
“Muna godewa Allah SWT saboda ƙanƙan da kansa, da tsoronsa ga Allah, da halinsa mai kyau."
Diyar Buhari na takaicin rasuwar mahaifinta
A baya, mun ruwaito cewa Noor Buhari, ɗiyar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta bayyana ɗimuwar da ta shiga bayan rashin mahaifinta.
Marigayi Buhari ya rasu yana da shekaru 82 a wani asibiti da ke birnin London, bayan fama da jinya, Sannan an birne shi a gidansa na Daura da ke jihar Katsina.
Ta ce rashin tsohon shugaban kasa wani babban gibi ne da ba za a iya cikewa ba, sannan za ta ci gaba da jin zafin rasuwarsa da tuna wa da shi har tsawon rayuwarta
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

