Bayan Suka daga 'Yan Arewa, Peter Obi Ya Fadi Dalilin Rashin zuwa Jana'izar Buhari

Bayan Suka daga 'Yan Arewa, Peter Obi Ya Fadi Dalilin Rashin zuwa Jana'izar Buhari

  • Wasu daga cikin ƴan Arewa da dama sun soki ɗan Peter Obi kan rashin halartar jana'izar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
  • Peter Obi ya fito ya bayyana cewa wasu matsaloƙi da suka sha .ƙarfinsa ne suka hana shi zuwa Daura don halartar jana'izar
  • Hakazalika ya nuna cewa bai makara ba domin ya je Daura a lokacin da ake ci gaba da yin zaman makoki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana dalilin rashin halartar jana’izar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Peter Obi ya ce bai halarci jana'izar Buhari ba ne da aka yi a Daura ranar Talata, saboda an taƙaita zirga-zirgar jiragen sama.

Peter Obi ya yi magana kan rasuwar Buhari
Peter Obi ya yi magana kan rashin zuwa jana'izar Buhari Hoto: @Mbuhari, @PeterObi
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce Peter Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai bayan ya je ta’aziyya ga iyalan marigayin a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

"An karya doka," Abin da Atiku ya yi ana jimamin rasuwar Buhari ya harzuƙa Ministan Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan isowar gawar Buhari daga Landan, an wuce da ita zuwa Daura inda aka yi masa jana'iza a ranar Talata.

Meyasa Peter Obi ƙin zuwa jana'izar Buhari?

Peter Obi ya ce ƙoƙarin da ya yi na halartar jana’izar ya ci tura saboda rashin jirage da kuma rufe filin jirgin saman Katsina domin ba wa manyan baki damar sauka.

"Eh, da wuya a zo nan jiya saboda babu jirage."
“Ko da kana da jirgi, ba za ka iya sauka a filin jirgin saman Katsina ba. An rufe shi gaba ɗaya saboda yawan manyan baƙi da za su halarci jana’izar."

- Peter Obi

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ƙara da cewa girmamawa ga mamaci ba sai ranar jana’iza ba, yana mai jaddada cewa ziyararsa har yanzu tana cikin lokacin alhini, rahoton TheCable ya tabbatar.

"Na yi imanin cewa za a ci gaba da makoki har yau da gobe. Duk wanda ya zo yau ko gobe, har yanzu yana cikin masu alhini ne."

Kara karanta wannan

Atiku ko Tinubu: Kungiya ta fadi wanda zai gaji kuri'un Buhari a Arewa

- Peter Obi

Peter Obi ya kare kansa kan jana'izar Buhari
Peter Obi ya wanke kansa kan rashin zuwa jana'izar Buhari Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Peter Obi ya tuna halayen Buhari

Peter Obi ya tuna mu’amalarsa da marigayi Buhari, musamman lokacin yaƙin neman zaɓensa, inda tsohon shugaban ƙasan ya shawarce shi da ya maida hankali kan kula da talakawan Najeriya.

“Na samu damar ganinsa a lokacin da nake yaƙin neman zaɓe, kuma har yanzu ina tunawa da maganarsa: ‘Don Allah ka kula da talakawan Najeriya’. Wannan ne nake tunawa kullum."
"Kuma ina da yaƙinin cewa ya yi iya ƙoƙarinsa gwargwadon ƙarfin da Allah ya ba shi. Ina tuna yadda roƙonsa kan jajircewa wajen yaƙi da kuma kula da talakawa."

- Peter Obi

An birne gawar Buhari a Daura

A wani labarin kuma, kun ji cewa an sada tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari da makwancinsa na ƙarshe a garin Daura.

Gawar Muhammadu Buhari dai an birne ta ne a gidansa bayan kammala yi masa sallar jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu na daga cikin waɗanda suka samu halartar jana'izar marigayin wacce aka gudanar a ranar Talata, 15 ga watan Yulin 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng