'Yan Bindinga Sun Hallaka Manoma Masu Yawa a Plateau
- Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'asa bayan sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya
- Ƴan bindigan sun hallaka manoma maza da mata a mummunan harin wanda suka kai a ƙaramar hukumar Riyom ta jihar
- Harin ya kuma yi sanadiyyar raunata wasu mutanen masu yawa bayan da ƴan bindigan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Ƴan bindiga sun hallaka aƙalla manoma 27, ciki har da maza da mata, a wani mummunan hari da suka kai a jihar Plateau.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a yankin Bindi-Jebbu da ke cikin ƙauyen Tahoss a ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Plateau.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Plateau
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutanen da dama sun jikkata a harin kuma an garzaya da su zuwa asibitoci daban-daban, ciki har da asibitin koyarwa na jami’ar Jos (JUTH) da asibitin Plateau.
Shugaban ƙungiyar matasan Berom (BYM) na ƙasa, Dalyop Solomon ya zargi wasu ƙungiyoyin Fulani masu ɗauke da makamai da kasancewa masu hannu a harin, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Ya bayyana yadda ƴan bindigan suka kutsa cikin ƙauyen a ranar Litinin, suna harbe-harbe ba kakkautawa tare da ƙone gidaje.
Shugaban BYM na ƙasa ya ce an adana dukkanin gawarwakin a asibitoci, kuma za a sanar da ranar jana’iza nan gaba.
“Mutane kusan 27 ne aka kashe, da kuma wasu da dama da suka jikkata. Mun kai gawarwakin zuwa asibitoci daban-daban kafin a kammala shirye-shiryen jana’izar su."
- Dalyop Solomon
Me hukumomi suka ce kan harin?
Shugaban ƙaramar hukumar Riyom, Bature Shuwa, ya tabbatar da faruwar harin amma bai iya faɗin adadin waɗanda suka mutu ba a lokacin da aka tuntuɓe shi.
Bature Shuwa ya bayyana cewa yana kan hanyarsa ta zuwa yankin da aka kai harin.
A wata hira ta wayar tarho, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Alfred Alabo, ya ce hukumar za ta fitar da cikakken bayani kan harin nan ba da daɗewa ba.
A halin da ake ciki, harin na ƙara ta’azzara matsalar tsaro da ke addabar jihar Plateau, musamman a ƙauyukan da ke fama da hare-haren ƴan bindiga.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga
- 'Yan Bindiga sun kashe matafiya a Zamfara, an yi awon gaba da wasu masu yawa
- Harin ƴan bindiga: Mutane sun ji azaba, sun fara tserewa daga gidajensu a Filato
- 'Yan sanda sun gwabza kazamin fada da ƴan bindiga a Nasarawa, an samu asarar rai
Ƴan bindiga sun sace malamin addinin Musulunci
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun sace wani malamin addinin musulunci a jihar Edo.
Ƴan bindigan sun sace babban limamin Uromi da ke ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas bayan ya fito daga gidansa.
Bayan sace babban limamin, sun kira iyalansa inda suka buƙaci a ba su N30m a matsayin kuɗin fansa kafin su sako shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

