"Babu Wani Ɓoye Ɓoye," Bagos Ya Faɗi Mutanen da Suka Ci Amanar Shugaba Buhari
- Dachung Bagos ya zargi wasu daga cikin mukarraban tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari da cin amana
- Tsohon ɗan Majalisar Wakilan Tarayya ya ce ƴan Najeriya sun yarda Buhari mai gaskiya ne, amma mutanen da ke kewaye da shi sun ci amanar da ya ba su
- Ya ce tsohon shugaban ƙasar ya yi bakin ƙoƙarinsa wajen gyara Najeriya amma rashin tsaro ya ƙaru a gwamnatinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Dachung Bagos, ya bayyana cewa wasu daga cikin mukarraban tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne suka ci amanarsa.
Hon. Bagos ya ce cin amanar da suka yiwa Marigayi Buhari ne ya haddasa “kara tabarbarewar cin hanci da rashawa” a lokacin mulkinsa.

Source: Facebook
Bagos ya bayyana haka ne a shirin Politics Today na Channels TV ranar Talata, jim kaɗan bayan kammala jana’izar tsohon shugaban a Daura, Jihar Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu muƙarraban Buhari sun ci amanarsa
“Idan muka duba Buhari a karan kansa, ya yi ƙoƙari ya zaƙulo wasu mutane da ya ɗauka za su taimaka masa wajen tafiyar da mulki kan gaskiya da adalci.
"Duk mun yarda cewa shi mutum ne mai gaskiya wanda ke nuna ba sani ba sabo a batun yaƙi da cin hanci da rashawa, amma yanzu wasu daga cikin hadimansa na fuskantar tuhumar rashawa."
"Wannan ya nuna cewa wasu daga cikin muƙarrabansa sun ci amanar da ya ba su a lokacin mulkinsa.
"A yau, batun cin hanci da rashin gaskiya a Najeriya ya ƙara muni, duk da ƙaddamar da tsarin Asusun Bai-ɗaya da ya yi domin inganta gaskiya da adalci.”
- Dachung Bagos.
Wane ƙalubale Buhari ya fuskanta a gwamnati?
Tsohon ɗan majalisar ya lura cewa rashin sa ido da kimanta ayyukan mukarraban Buhari na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka addabi gwamnatinsa.
"Kula da ayyuka da sa ido kan mukarrabansa a wancan lokaci ya kasance babban ƙalubale a gare shi, la'akari da cewa ya yarda da su kuma ya basu amana,” in ji shi.

Source: Facebook
Bagos ya amince cewa Buhari ya shahara a matsayin mutum mai gaskiya, amma matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar nan a mulkinsa babban abin damuwa ne.
A rahoton Punch, ya ci gaba da cewa:
“Buhari ya kasance ana kallonsa a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana. Gaskiyar magana ita ce, matsalar rashin tsaro ita ce babbar barazana da ta addabi mulkinsa a matsayin shugaban ƙasa.
"Amma a matsayin mutum, kowa yana son yin ƙoƙari da gwada bakin ƙarfinsa. Shugaban ƙasa ya ce Buhari ya yi iya ƙoƙarinsa, amma hakan bai wadatar ba."
An nemi Tinubu ya ƙara karrama Buhari
A wani labarin, kun ji cewa wani jigo a APC, Dr Aliyu Ibrahim, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sanya sunan Muhammadu Buhari a wani muhimmin wuri na ƙasa.
Ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da adalci da kuma wanzar da tarihin Buhari a zuciyar ‘yan Najeriya.
Dr Aliyu ya ce sanya sunan tsohon shugaban kasa a wata hanya, titi, filin jirgi ko wata cibiyar gwamnati zai taimaka wajen tuna hidimar da ya yi wa ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

