Ana Ci Gaba da Bayyana Ayyukan Alheran Buhari, Malami Faɗi Abin da Ya Sani
- Tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami ya ce rashawa ba ta samu gurbi a mulkin marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba
- Ya bayyana haka ne a lokacin da kasa ke alhinin rashin Buhari da wasu ke zargi da karya umarnin kotuna daban-daban a lokacin mulkinsa
- A kariyar da ya ba gwamnatinsu, Malami ya nanata cewa tsohon shugaban ya yi duk abin da zai iya wajen bin doka da hana wawashe kudin jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana yadda marigayi Muhammadu Buhari ya jagoranci gwamnatin sa.
Ya fitar da wasu bayanai a kan yadda tsohon shugaban ya zage damtse wajen samun nasara a yaki da rashawa da rage yawan wawason kudin gwamnati.

Source: Facebook
Arise News ta wallafa cewa ya ce rashawa ba ta samu wurin zama a gwamnatin Buhari ba, yayin da aka samu nasara a manyan shari’o’in da suka shafi rashawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari ya yaki rashawa, cewar Malami
Daily post ta ruwaito Malami ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta samu nasarar kwato kadarori da suka haura $2bn.
A cewarsa:
“Ko wane mizani aka yi amfani da shi, Buhari ya cimma nasarori masu tarin yawa wajen yaki da rashawa.”
Malami ya lissafo wasu daga cikin hanyoyin da gwamnatin Buhari ta samar domin magance salwantar kuɗin gwamnati.
Ya ce kadan daga cikinsu sun hada da samar da asusun bai ɗaya na tarayya wato TSA da kuma bijiro da lambar tantance banki da aka fi sani da BVN don hana zurarewar kudi.
Yadda Buhari ya yi zarra a yakar rashawa
Malami ya bayyana cewa Muhammadu Buhari ya samu karramawa daga Tarayyar Afrika (AU), wadda ta nada shi jakadan yaki da rashawa a nahiyar.
Haka kuma, Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da Miyagun Ɗanyoyi da Laifuka (UNODC) ta yaba da irin salon gwamnatinsa wajen yakar rashawa.
Duk da cewa wasu na zargin gwamnatin Buhari da kare abokan siyasa da kin bin umarnin kotu, Malami ya musanta hakan.

Source: Facebook
Ya ce gwamnatin Buhari ta yi aiki ne bisa doka da tsarin mulkin ƙasa a dukkanin abubuwan da aka aiwatar a zamanin tsohon shugaban.
Malami ya ce:
“Buhari bai taba wuce gona da iri ba wajen tafiyar da mulki. Duk wani abu da aka yi, bisa doka da kundin tsarin mulki ne.”
Radda ya gigita da rasuwar Buhari
A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya samu halarta a jana’izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, inda aka ga gwamnan yana zubar da hawaye.
Gwamna Radda ya kasa jure wa alhinin rasuwar tsohon shugaban kasar a daidai lokacin da ake shirin sanya shi a cikin kabarinsa, wanda ya zama makwancinsa na karshe a duniya.
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025, a wani asibiti da ke birnin London, ƙasar Birtaniya bayan ya sha fama da jinya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

