Jigon APC Ya Fadi Babbar Girmamawar da Ta Rage Tinubu Ya Yi wa Buhari

Jigon APC Ya Fadi Babbar Girmamawar da Ta Rage Tinubu Ya Yi wa Buhari

  • Dr Aliyu Ibrahim ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya sanya sunan Muhammadu Buhari a wata muhimmiya cibiyar kasa
  • Jigo a jam'iyyar APC ya ce hakan zai taimaka wajen tunawa da gudunmawar Buhari ga ci gaban Najeriya
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne a London kuma an birne shi a Daura, Katsina, ranar Talata 15 ga Yuli, 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, FCT – Wani jigo a jam’iyyar APC, Dr Aliyu Ibrahim, ya bukaci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sanya sunan marigayi Muhammadu Buhari a wata muhimmiya cibiyar kasa.

Dr Aliyu da ya ke jagoran kungiyar National Agenda For Tinubu 2027 (NAFT.27) ya bukaci hakan ne domin girmama Buhari da kuma tuna irin gudunmawar da ya bayar ga Najeriya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda aka fito da gawar Buhari daga jirgi da manyan mutanen da aka gani

shugaba Bola Tinubu yayin karbar gawar Buhari a Katsina
shugaba Bola Tinubu yayin karbar gawar Buhari a Katsina. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce Dr Aliyu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, bayan birne Buhari a gidansa da ke Daura, jihar Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da adalci da kuma wanzar da tarihin Buhari a zuciyar ‘yan Najeriya.

Aliyu: 'Buhari ya sadaukar da kansa ga kasa'

Dr Aliyu ya ce sanya sunan tsohon shugaban kasa a wata hanya, titi, filin jirgi ko wata cibiyar gwamnati zai taimaka wajen tuna jajircewarsa da sadaukarwa da ya yi wa kasar.

Jigon APC ya ce:

“Buhari ya nuna jajircewa da kwazo wajen bai wa Najeriya gudunmawa ta fuskar siyasa da shugabanci.
"Duk da shan kaye sau uku a zaben shugaban kasa, ya ci gaba da gwagwarmaya har sai da ya samu nasara a 2015, bisa taimakon kwararren dan siyasa, Bola Ahmed Tinubu.”

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

An gano bidiyon Aisha Buhari tana rusa kuka a gaban Shettima yayin da ya ke ta'aziyya

“Wannan ne ya sa Buhari ya zama daya daga cikin shugabannin da suka fi shahara a tarihin siyasar Najeriya.
"Don haka yana da kyau Shugaba Tinubu ya nuna godiya da girmamawa ta hanyar sanya sunansa a wani wuri ko abu da zai dawwama.”

Ana cigaba da tuna Buhari bayan rasuwa

An birne Muhammadu Buhari ne a ranar Talata, 15 ga Yuli, a Daura, jihar Katsina, bayan rasuwarsa a asibiti da ke London.

Bikin jana’izar ya tara manyan shugabanni daga sassa daban-daban na kasar ciki har da Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima.

Sauran sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa’i, Aminu Tambuwal da Sarki Aminu Ado Bayero.

Yadda aka yi wa Buhari sallar gawa daga nesa a Gombe
Yadda aka yi wa Buhari sallar gawa daga nesa a Gombe. Hoto: Bashir Ahmad|Aminu Malam
Source: Facebook

Wasu daga cikin mahalarta jana’izar sun bayyana Buhari a matsayin jagora mai gaskiya, wanda ya sadaukar da rayuwarsa don kyautata Najeriya.

A yanzu dai za a duba ko kiran Dr Aliyu Ibrahim na neman a sanya sunan Buhari a wata muhimmiya cibiyar kasa zai samu karbuwa.

An yi mafarkin Buhari ya shiga aljanna

Kara karanta wannan

'Akwai alaƙa mai kyau tsakaninsu': Bidiyon haɗuwar Buhari da Tinubu na ƙarshe

A wani rahoton, kun ji cewa an yi mafarkin shugaba Muhammadu Buhari ya shiga aljanna kwana daya bayan birne shi.

Wani hadimin gwamnan Yobe, Sheriff Almuhajir ne ya bayyana cewa ya yi mafarkin a wani sako da ya fitar a yau Laraba.

Sai dai mutane da dama sun bayyana ra'ayoyi kan maganar mafarki kuma Legit Hausa ta tattaro abin da suka fada a wannan rahoton.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng