Malamin Jami'a Ya Yi Mafarkin Shugaba Buhari Ya Shiga Aljanna

Malamin Jami'a Ya Yi Mafarkin Shugaba Buhari Ya Shiga Aljanna

  • Sheriff Almuhajir ya bayyana cewa ya yi mafarkin ganin marigayi Muhammadu Buhari cikin Aljanna
  • Malami a jami'ar jihar Yobe ya bayyana hakan ne bayan birne tsohon shugaban kasa a Daura, jihar Katsina
  • Maganar mafarkin ta jawo martani da ra’ayoyi masu bambanta daga mabiyansa a kafafen sada zumunta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe – Malamin jami'a kuma hadimin gwamnan jihar Yobe, Sheriff Almuhajir, ya bayyana cewa ya yi mafarkin ganin marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin Aljanna.

Almuhajir ya bayyana haka ne a yau Laraba, bayan da aka yi jana’izar Buhari a gidansa da ke Daura, jihar Katsina a ranar Talata.

Sheriff Almuhajir daga jihar Yobe ya yi mafarkin Buhari a Aljanna
Sheriff Almuhajir daga jihar Yobe ya yi mafarkin Buhari a Aljanna. Hoto: Bashir Ahmad|Sheriff Almuhajir
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa Sheriff Almuhajir da ya koyar da ilimin addinin Musulunci a jami'ar Yobe ya wallafa sakon yin mafarkin a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Yadda aka binne gawar Muhammadu Buhari a Daura

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, a birnin London bayan fama da jinya.

Almuhajir ya wallafa sakon nasa da kamar haka:

“Wallahi na yi mafarkin Buhari ya shiga Aljannah,”

Martani kan mafarkin Buhari a aljanna

Bayan bayyana mafarkin, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu ta kafafen sada zumunta, wasu suna goyon baya yayin da wasu kuma ke bayyana shakku.

Wani daga cikin masu martani, Imam Sani, ya ce:

“Allah ya tabbatar. Ameen. Kuma kai ma Allah yayi maka ƙarshe mai kyau da sakamakon Aljannah.”

Haka nan Ibrahim Aliyu Tahir ya ce:

“Ya Allah ka yafe mana gaba ɗayan mu. Kowa mai laifi ne. Idan ba ka yafewa Buhari ba, to ka daina zagin shi, saboda kada ciko ya biyo gyartai.”
Lokacin da Bola Tinubu ya karbi gawar Buhari a Katsina
Lokacin da Bola Tinubu ya karbi gawar Buhari a Katsina. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Wasu sun nuna shakku a kan mafarkin

Daya daga cikin masu martani, Abban Adawiyya Alharazumy, ya ce:

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda aka fito da gawar Buhari daga jirgi da manyan mutanen da aka gani

“Wannan shi ake kira da rudani. Kaima kasan karya ka gani kawai, zuciyarka tana saka maka abin da ba ka da tabbacin sa ne.”

Haka nan Muhammad Aliyu ya kara da cewa:

“Mafarki kala-kala ne kuma ba kowane mafarki ne gaskiya ba. Wani mafarkin magagin barci ne.”

Sai dai wasu kamar Lawan Alhaji Umaru sun karfafa mafarkin, inda ya ce:

“Abin yana ranka, shi ya sa. Allah ya tabbatar da hakan. Wannan ba komai ba ne a wajen Mahaliccinmu Mai iko da komai.”

Aisha M. Kazimiyyah ta ce:

“Toh Dr, ai daman abin da ka sa a rai shi ake gani a mafarki. Idan ka ci nama kafin barci, kana iya mafarkin kana ci.
“Tun da yaƙinin ka ya gaskata maka, ina addu’a Allah ya saka a makoma ɗaya da Buharin, domin ni mai maka fatan shiga Aljanna ce har rai na.

Amina Mohammed ta yaba wa Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya, Amina Mohammed ta yi jinjina ga Muhammadu Buhari.

Amina Mohammed ta bayyana cewa shugaba Buhari ne ya karfafa mata gwiwa wajen tafiya aiki majalisar dinkin duniya.

Baya ga haka, Hajiya Amina ta ce akwai darusa da dama da 'yan Najeriya za su koya a rayuwar marigayi Muhammadu Buhari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng