Buhari: Diyar Tsohon Shugaban Kasa Ta Fadi Halin da Ta Shiga bayan Rasuwar Mahaifinta

Buhari: Diyar Tsohon Shugaban Kasa Ta Fadi Halin da Ta Shiga bayan Rasuwar Mahaifinta

  • Noor, ɗiyar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ta bayyana baƙin cikin da ta shiga bayan rasuwar mahaifinta, a Landan da ke Burtaniya
  • Tsohon shugaban ƙasa Buhari ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a asibiti da ke birnin London, yana da shekara 82, kuma an binne shi a gidansa na Daura
  • Jama’a a sassa daban-daban na Najeriya, ciki har da Bauchi, na ci gaba da gudanar da addu’o’in nema wa tsohon shugaban rahamar Allah Subhanahu wa Ta'ala

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Noor, ɗiyar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ta bayyana yadda ta ji ɗacin rai da ta shiga bayan rasuwar mahaifinta a yammacin Lahadi.

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025 yana da shekara 82 a wani asibiti da ke birnin London.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Yadda aka binne gawar Muhammadu Buhari a Daura

Diyar tsohon shugaban kasa, Noor tare da marigayi Buhari
Noor ta shiga alhinin rashin mahaifinta Hoto: @noorbuhari
Source: Twitter

Ta cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Litinin, Noor ta bayyana yadda rasuwar tsohon shugaban kasar ta yi mata yankan kauna.

Noor ta kadu da rasuwar Buhari

Jaridar Punch ta wallafa cewa Noor ta bayyana yadda mutuwa ta kawo karshen duk wasu abubuwan da ta shirya tsakaninta da mahaifinta, wadanda ta so su yi tare kafin ya amsa kiran Mahalicci.

A sakon da ta wallafa, ta ce:

"Zuciyata cike take da baƙin ciki saboda ba za mu samu damar ci gaba da kasancewa tare ba da kuma gudanar da abubuwan da na tsara mana ba.
Zan ci gaba da tunaninka har abada. Ina addu’a Allah Ya ba ka matsayi mafi girma a Aljanna, kuma ruhinka ya huta cikin salama madawwami, Daddy."

Ana ci gaba da alhinin rasuwar Buhari

Sakon Noor ya taɓa zuciyar mutane da dama, wanda ya kara jaddada yadda jama'a ke alhinin rasuwar tsohon shugaban kasar.

Kara karanta wannan

An tafi da gawar Buhari zuwa mahaifarsa Daura bayan ta iso Najeriya

Jama'a na ci gaba da mika ta'aziyyar rasuwar Buhari a sassa daban-daban na kasar nan bayan an birne shi a gidansa na Daura da ke jihar Katsina.

Tsohon shugaban kasa, Buhari
Jama'a na ci gaba da roka wa Buhari rahamar Allah SWT Hoto: Muhammadu Buhari
Source: UGC

A jihar Bauchi, wata makarantar Islamiyya ta gudanar da addu’o’in kwanaki uku domin nema wa tsohon shugaban rahama, wanda ke nuna yadda jama'ar Arewacin kasar nan su ke girmama tsohon shugaban.

Buhari ya yiwa jama'a hidima a zamanin soja da shugabancin farar hula, inda ya bar tarihi, duk da cewa akwai masu ra'ayi na daban a kan salon jagorancinsa.

AbdulSalami ya yi jimamin rasuwar Buhari

A baya, kun samu labarin cewa tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya bayyana yadda suka yi jinya tare da marigayi Muhammadu Buhari a Landan.

Abdulsalami ya ce dangantakarsa da Buhari ta fara ne tun shekarar 1962, lokacin da suka shiga rundunar sojin Najeriya tare, kuma tun daga wancan lokacin suka ci gaba da kasancewa tare.

A yayin da yake tuna rayuwar Buhari da halayyarsa, Abdulsalami ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai hankali, kwantar da hankali da kuma cikakken rikon amana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng