Babbar Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi wa Buhari Shaida Mai Kyau

Babbar Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi wa Buhari Shaida Mai Kyau

  • Amina Mohammed ta ce marigayi Shugaba Muhammadu Buhari bai ji dadin siyasa ba, ya jure harkar ne saboda kishin ƙasa
  • Tsohuwar ministar muhallin ta ce Buhari ne ya bada goyon baya ta koma Majalisar Ɗinkin Duniya bayan ta ce ba za ta je ba
  • Amina Mohammed ta bayyana cewa Buhari ya dage a kan adalci da shugabanci na gaskiya har zuwa ƙarshen mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakiyar sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), Hajiya Amina Mohammed, ta bayyana cewa marigayi shugaba Muhammadu Buhari ya kasance mutum mai ƙaunar ƙasarsa.

Hajiya Amina Mohammed ta ce duk da cewa ba ya jin daɗin harkokin siyasa, ya shiga ciki ne saboda kishin kasa.

Amina Mohammed a zaune tare da Muhammadu Buhari
Amina Mohammed a zaune tare da Muhammadu Buhari. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Amina ta bayyana haka ne cikin wata hira da aka yi da ita a tashar Channels TV, inda ta ƙara da cewa Buhari ya zama alamar juriya da kishin ƙasa da sadaukarwa.

Kara karanta wannan

Buhari: Diyar tsohon shugaban kasa ta fadi halin da ta shiga bayan rasuwar mahaifinta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, a wani asibiti da ke birnin London, kuma aka birne shi a ranar Talata a gidansa da ke Daura, jihar Katsina.

Yadda Buhari ya ƙarfafa Amina zuwa UN

Amina ta ce lokacin da ta ke yi wa gwamnatin Buhari aiki a matsayin ministar muhalli, wani babban jami’i UN ya shaida mata cewa za a nemi ta koma aiki a Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ta bayyana cewa:

"Mun zauna a wani taro a Marrakesh lokacin taron sauyin yanayi, sai Ban Ki-moon ya ce za a iya nemana na zama mataimakiyar sabuwar sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya.
"Sai na ce, 'Ba zai yiwu ba. Na dawo gida ne domin na yi wa Najeriya hidima.'"

A cewarta, ta je wurin Buhari don neman goyon bayansa domin ta ki amincewa, amma daga baya ya ƙarfafa ta da ta karɓi aikin.

Amina a taron majalisar dinkin duniya
Amina a taron majalisar dinkin duniya. Hoto: Amina J. Mohammed
Source: UGC

Buhari bai jin daɗin siyasa inji Amina

Kara karanta wannan

Mutanen Daura sun fadi yadda Buhari ya rayu a tsakaninsu bayan sauka a mulki

A cikin hirar, Amina Mohammed ta ce shugaba Buhari ya sauya daga soja zuwa tsarin dimokuraɗiyya da niyyar kawo sauyi.

The Cable ta wallafa cewa ta ce:

“Buhari bai ji dadin da harkokin siyasa ba, amma ya dage ne saboda kishin ƙasa. Ya yi takara da yawa, kuma Allah ya nufa ya zamo shugaban ƙasa a lokacin da ya dace.”

Ta ƙara da cewa Buhari mutum ne da ke girmama doka da oda, kuma duk da cewar tsarin siyasa ba cikakke ba ne, ya yarda ya yi amfani da shi don ciyar da ƙasa gaba.

Darasin da za a koya a rayuwar Buhari

Amina ta ƙara da cewa darasin da Buhari ya bar wa ‘yan Najeriya shi ne kada su taɓa daina ƙoƙarin gina ƙasarsu.

Ta ce:

“Kamar yadda Buhari ya fahimta, ci gaba ba ya zuwa cikin dare ɗaya. Ya koyar da cewa akwai matsaloli a Najeriya, amma mu ne za mu gyara ta.
“Wani lokaci yana jin daɗin ganin yadda matasa ke kwazo, amma wasu lokuta kuma yana jin takaici idan mutane sun gaza fahimtar inda yake son su je da ƙasa.”

Kara karanta wannan

Mutuwar Buhari ta girgiza Buba Galadima, ya ce ya yafe masa abin da ya faru a baya

An yi wa Buhari sallar gawa a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa daruruwan mutane sun yi wa marigayi shugaba Muhammadu Buhari sallar gawa a Gombe.

An yi wa Buhari sallar gawa daga nesa ne a lokacin da ake kokarin zuwa da gawar shi Daura na jihar Katsina.

Wasu da suka halarci sallar gawar a Gombe sun bayyana wa Legit Hausa cewa sun je jana'izar ne domin yi wa Buhari addu'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng