Bidiyo: Yadda Aka Fito da Gawar Buhari daga Jirgi da Manyan Mutanen da Aka Gani
- Filin jirgin Katsina ya cika da jama'a yayin da aka kawo gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga London
- Shugaba Bola Tinubu, Kashim Shettima, da iyalai da 'yan uwan Buhari da kuma manyan jami'an gwamnati suka tarbi gawar
- An ce gwamnoni 20, ministoci, da shugabannin siyasa ne suka hallara a Daura, inda za a yi jana'iza tare da binne gawar Buhari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina – Filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ya cika ya batse yayin da aka kawo gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari domin fara tafiyarsa ta karshe zuwa Daura.
Cikin tsananin alhini, gwamnoni, ministoci, da fitattun mutane daga sassa daban-daban na ƙasar suka hallara domin karrama Buhari wanda shugabancinsa ya yi tasiri ga Najeriya.

Source: Twitter
Tinubu ya karbi gawar Buhari a Katsina
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya, inda aka ganshi a sahun gaba wajen karbar gawar daga cikin jirgi, kamar yadda aka gani a wani bidiyo da @Imranmuhdz ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon an ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya rako gawar daga Landan, tare da wasu fitattun jami'an gwamnati da suka taho tare.
Haka kuma, Yusuf Buhari, ɗan marigayin shugaban kasa, yana tare da su.
Uwargidan shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu, ta kasance cikin mahalarta wannan taro, abin da ke nuna hadin kan shugabannin Najeriya wajen karrama Buhari.
Gwamnoni da ministoci sun tarbi gawar Buhari
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya karɓi baki, musamman ma takwarorinsa daga wasu jihohin, a matsayin babban mai masaukin baki.
Gwamnoni daga sassa daban-daban na ƙasar sun halarta domin yin bankwana da Buhari, ciki har da gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu; na Ogun, Dapo Abiodun; na Borno, Babagana Zulum; da na Zamfara, Dauda Lawal.
Rahotanni sun nuna cewa aƙalla gwamnoni 20 ne suka samu halarta ko ake sa ran isowarsu, abin da ke nuna girman mutunci da girmamawar da ake yi wa Buhari a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Iyalai na hawaye, Shugaba Tinubu ya karɓi gawar Muhammadu Buhari a Katsina
A bangarorin ministoci, akwai ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, da na kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Abubakar Bagudu, sun isa inda suka karɓi Firayim Ministan Nijar, Ali Lamine Zeine — wanda ya zama shugaban ƙasa na farko daga wata ƙasa da ya iso.
An ga ministan watsa labarai, Mohammed Idris, wanda ke da alhakin shirya jana’izar. Haka kuma an ga ministan noma Sanata Abubakar Kyari a wajen karɓar gawar.

Source: Twitter
An ga 'yan siyasa da manyan 'yan kasuwa
Fitattun mutane da suka halarta sun hada da manyan jiga-jigan Najeriya, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Sauran sun hada da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da mataimakinsa, Sanata Jibrin Barau; da kuma kakakin majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, wanda ya kasance kusa da Buhari a lokacin mulkinsa, ya tsaya da nutsuwa a wajen taron, inji rahoton Tribune.s
Shahararrun ’yan kasuwa da tsofaffin ministoci kamar Aliko Dangote, Lai Mohammed da Rotimi Amaechi sun halarta, tare da fitattun mutane daga Katsina irinsu Dahiru Mangal duk sun hallara.
An kuma ga tsofaffin gwamnoni kamar Nasir El-Rufai, Yahaya Bello, da Ibikunle Amosun, da tsohon shugaban ma’aikata Ibrahim Gambari, da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika.
Kalli bidiyon a nan kasa:
Saudiyya, Amurka sun magantu kan rasuwar Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an rufe ofisoshin jakadancin Amurka da ke Abuja da Legas a ranar Talata domin girmama rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
A bangare guda kuma, Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya aike da sakon ta’aziyya zuwa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da wannan babban rashi.
Marigayi Muhammadu Buhari ya rasu ne a asibiti da ke birnin London a ranar 13 ga watan Yuli, 2025, bayan doguwar jinya da ya sha fama da ita.
Asali: Legit.ng

