Shugaba Tinubu Ya Dura Jihar Katsina ana Dakon Ƙarasowar Gawar Buhari
- Mai girma shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Katsina yayin da ake shirye-shiryen jana'izar magabacinsa, Muhammadu Buhari
- Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa da jami'an gwamnatinsa da takwarorinsa na wasu jihohi sun tarbi Bola Tinubu a filin jirgin sama
- A halin yanzu dai ana dakon ƙarisowar tawagar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya ɗauko gawar Buhari daga Landan zuwa Katsina
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya isa jihar Katsina a wani bangare na shirye-shirye jana'izar marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Ana sa ran Shugaba Tinubu da kansa ne zai karɓi gawar Buhari a Katsina domin girmamawa ta musamman gabanin a wuce da ita zuwa Daura.

Source: Facebook
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ya tabbatar da isowar Shugaba Tinubu a wani gajeren saƙo da ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun jiya dai Bola Ahmed Tinubu ya turo ministoci da manyan kusoshin gwamnatinsa zuwa Daura domin tsara jana'izar ban girma ga Buhari.
Shirye-shiryen jana'izar Buhari sun kankama
Ƙarisowar Shugaba Tinubu na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ake dako domin shirin jana’izar ƙasa ta girmamawa da za a gudanar a Daura, garin da marigayin ya fito.
A Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Umaru Musa Yar’adua, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya tarbi Shugaban Tinubu tare da wasu manyan jami’an gwamnati da shugabannin siyasa.
Daga cikin waɗanda suka halarta domin tarbar shugaban ƙasa akwai Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun.
Gwamnonin da suka je tarbar Shugaba Tinubu
Haka kuma wasu gwamnoni daga jihohin ƙasar nan sun je wurin tarbar Tinubu, ciki har da AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF).
Sauran gwamnonin sun haɗa da Mai Mala Buni na Yobe, Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe, Umar Namadi na Jigawa, Dr. Nasir Idris na Kebbi, da Dauda Lawal na Zamfara.

Source: Facebook
Ahmed Aliyu na Sokoto, Babajide Sanwo-Olu na Legas, Dapo Abiodun na Ogun, Monday Okpebholo na Edo, Hope Uzodimma na Imo, da Bassey Edet Otu na Kuros Riba suna wurin.
Ana sa ran kowane lokaci gawar Buhari za ta ƙariso kuma Shugaba Tinubu zai karɓe ta, sannan ya yiwa wannan tawaga jagoranci zuwa Daura wurin birni marigayin.
Tinubu ya naɗa kwamitin jana'izar Buhari
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kwamitin ministoci da manyan jami'an gwamnti domin shirya jana'izar Muhammadu Buhari a Daura.
Tinubu ya ɗora wa kwamitin, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, zai jagoranta, alhakin tsarawa da gudanar da jana’izar da ta dace da darajar marigayi Buhari.
Kwamitin ya ƙunshi ministoci 10 da manyan jami'an gwamnatin Najeriya ciki har da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da wasu hadimai.
Asali: Legit.ng

