An Fadi Lokacin da Ake Sa Ran Birne Muhammadu Buhari a Daura
- Tuni aka kara inganta tsaro tsakanin Katsina da Daura yayin da ake shirin birne tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a gidansa
- Tun safiyar yau Litinin ne tawagar gwamnatin tarayya da Kashim Shettima ya ke jagoranta ke hanyar taho wa da gawar tsohon shugaban kasar
- Shirye-shirye sun yi nisa, yayin da aka fara tona makwancin tsohon shugaban da ake sa ran za a rufe bayan an yi masa sutura a Daura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – An ƙarfafa matakan tsaro a gidan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da ke Daura a jihar Katsina, yayin da ake sa ran isowar gawarsa daga birnin Landan.
Gawar marigayin da tuni ta taso daga Birtaniya a cikin jirgin rundunar sojin saman Najeriya, na kan hanyarta zuwa gida.

Source: Getty Images
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa ana sa ran za a sauke gawar a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu zai karbi gawar Buhari
Rahoton ya kara da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne da kansa zai karɓi gawar da zarar Kashim Shettima da shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila sun sauko da ita.
Wadannan manyan jami’an gwamnatin tarayya suna cikin tawagar da ta dawo da gawar daga Birtaniya.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), sojojin Najeriya, ’yan sanda, da jami’an tsaron fararen hula (NSCDC) sun yi cikar kwari a gidan.

Source: Twitter
Jami'an tsaron, wadanda suka bazu a manyan wurare na aikin tabbatar da tsaro yayin da ake jiran isowar gawar Buhari.
Tuni aka fara tona kabari a wani ɓangare na gidan domin birne marigayin bayan isowarsa daga daga Landan.
Yaushe za a birne Buhari?
Rahotanni daga cikin gida sun bayyana cewa, da zarar gawar Muhammadu Buhari ta iso Daura, za a yi masa sutura da Azahar, kafin birne shi a cikin gidansa.
A halin yanzu, an ƙarfafa tsaro a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, inda aka ƙaddamar da matakan tsaro masu tsauri.
Daga cikin matakan da aka dauka akwai kafa shingayen bincike fiye da 12 daga garin Katsina har zuwa Daura domin tabbatar da tsaro.
Marigayi Buhari, wanda ya shugabanci Najeriya a matsayin shugaban soja a shekarun 1980 da kuma zababben shugaban ƙasa daga 2015 zuwa 2023, ya rasu ne ranar Lahadi.
Buhari: Kwamitin Tinubu ya sauka a Daura
A wani labarin, kun ji cewa kwamitin gwamnatin tarayya da aka kafa domin shirya jana’izar marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sauka a Jihar Katsina da safiyar Talata.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya kafa kwamitin na musamman, domin jagorantar dukkannin shirye-shiryen jana’izar cikin tsari da girmamawar da ta kamaci tsohon shugaban.
Kwamitin yana da alhakin tsara dukkannin abubuwan da suka shafi jana’izar marigayin, ciki har da tsarin tafiyar da jana’iza da haɗin gwiwar hukumomin gwamnatin Katsina da iyalansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
