Shugabannin Kasashen Duniya Sun Fara Isowa Najeriya domin Halartar Jana'izar Buhari
- Wakilin shugaban Jamhuriyar Nijar kuma Firaministan kasar, Ali Lamine Zeine ya dura a Katsina domin halartar jana'izar Muhammadu Buhari
- Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa da wasu daga cikin ƴan kwamitin shirya jana'izar ne suka tarbe shi a filin jirgin sama yau Talata
- Har yanzu dai ana ci gaba da dakon isowar tawagar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima wanda ya ɗauko gawar Buhari daga Landan zuwa gida
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya tarbi Firaministan Jamhuriyar Nijar, Ali Lamine Zeine, a garin Katsina.
Wannan dai wani bangare na shirin jana’izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu ranar Lahadi da ta gabata a wani asibiti a birnin Landan.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulaha Mohammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin duniya za su zo jana'izar Buhari
Ana sa ran bayan Firaministan Jamhuriyar Nijar mai maƙwaftaka da Najeriya, akwai wasu shugabannin duniya da za su halarci jana'izar Muhammadu Buhari.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya tarbi Firministan tare da wasu manyan kusohin gwamnatin tarayya da ta jiha a filin sauka da tashin jiragen sama na Katsina.
Daga cikin waɗanda suka halarci tarbar har da Mataimakin Gwamnan Katsina, Faruk Lawal Jobe da Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare na Ƙasa, Sanata Atiku Abubakar Bagudu.
Sauran sun haɗa da da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Jama'a, Mohammed Idris Malagi; tare da wasu manyan jami’an gwamnatin Jamhuriyar Nijar.
Wannan tawaga ƙarƙashin jagorancin Ali Lamine Zeine ita ce za ta wakilci Jamhuriyar Nijar a wurin jana'izar Muhammadu Buhari.
Manyan baki sun fara cika jihar Katsina
A yau Talata, 15 ga watan Yuli, 2025 za a yi wa Buhari sutura a kai shi makwancinsa a Daura da ke jihar Katsina a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Bayan tawagar gwamnatin Nijar, ana sa ran wasu shugabannin ƙasashen Afirka za su halarci jana'izar Buhari a Daura da ke Katsina.

Source: Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ayyana hutu a ranar Talata domin bai wa ‘yan Najeriya damar halartar jana’izar Buhari, wanda ya shugabanci ƙasar daga 2015 zuwa 2023.
Tuni dai manyan ƙusoshin gwamnatin Najeriya kama daga ministoci, hadiman shugaban ƙasa da kuma gwamnoni suka taru a Katsina domin bankwana da Buhari.
Jama'a sun yiwa Buhari Salatul Ghaib a Gombe
A wani labarin, kun ji cewa dandazon jama'a sun fito sun yi wa Muhammadu Buhaɗi sallar jana'iza duk da babu gawarsa a Gombe domin roƙa masa Allah gafara.
Jama'a sun yi wa Buhari Salatul Ghaib, watau yiwa mamaci sallar janaza ba tare da gawarsa ba da misalin ƙarfe 11:00 na safe a yau Talata, kafin a birne tsohon shugaban kasar a Daura.
Mahalarta sallar sun bayyana cewa hakan na daga cikin al’adun Musulunci domin nuna alhini da roƙon rahamar Allah ga mamacin, musamman idan ya rasu a wani wuri daban.
Asali: Legit.ng

