Tawagar Shugaban Kasa Ta Sauka a Katsina kan Shirin Birne Buhari

Tawagar Shugaban Kasa Ta Sauka a Katsina kan Shirin Birne Buhari

  • Kwamitin gwamnatin tarayya kan shirya jana’izar gwamnati ya isa jihar Katsina don tsara birne marigayi Muhammadu Buhari
  • Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima na jagorantar dawo da gawar Buhari daga Birtaniya domin yi masa sutura a gida
  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ayyana zaman makokin kwanaki bakwai, yayin da ya umarni a sassauko da tutocin ƙasar don girmama Buhari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Kwamitin shugabancin tarayya da aka kafa don shirya jana’izar marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sauka a jihar Katsina.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya kafa kwamitin domin kula da dukkannin shirye-shiryen jana’izar tare da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina da iyalan marigayin.

Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Tawagar tsohon shugaban kasa ta isa Katsina Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Tsare-Tsaren Ƙasa, Mohammed Idris, ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Shugabannin ƙasashen duniya sun fara isowa Najeriya domin halartar jana'izar Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar shugaban kasa ta sauka a Katsina

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa isowar kwamitin na zuwa ne bayan tashi da gawar marigayi Buhari daga Landan a cikin jirgin sama mallakin rundunar sojin saman Najeriya.

Shugaban kwamitin, Sakatare Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, CON ne ya jagoranci tawagar zuwa Katsina safiyar Talata.

Sauran 'yan kwamitin sun haɗa da Ministan Kuɗi da kuma wanda ke jagorantar tattalin arziki, da kuma Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki.

Ana jiran Kashim Shettima a Katsina

Yayin da tawagar gwamnatin tarayya ke jiran isowar gawar a Katsina, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ke jagorantar tawaga daga Birtaniya don dawo da gawar Buhari gida.

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Ana jiran gawar Muhammadu Buhari Hoto: Muhamadu Buhari
Source: Getty Images

An dora wa kwamitin, wanda Sakatare Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya shugabanta, alhakin tsara da aiwatar da shirin jana’izar da ta dace da matsayin marigayin.

A cewar Ministan, kwamitin yana aiki tare da gwamnatin jihar Katsina da iyalan marigayi domin tabbatar da cewa an shirya komai yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

An yi wa Buhari sallar jana'iza a Gombe yayin da ake jiran gawar shi a Daura

Addu'ar Mohammed Idris ga Buhari

Mohammed Idris ya yiwa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari addu'ar Allah Ya yafe masa dukkanin kura-kuransa.

Ya kara da cewa tuni aka ci gaba da shiri da kwamitin gwamnatin Katsina domin tabbatar da an yi wa Buhari sutura irin ta manya.

Haka kuma, Shugaba Tinubu kuma ya ayyana kwanaki bakwai na zaman makoki a fadin kasa, daga ranar Lahadi, 13 ga Yuli, inda aka umarci a saukar da tutocin ƙasa.

An fara shirin birne Buhari

A wani labarin, mun wallafa cewa an ƙarfafa matakan tsaro a gidan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da ke Daura a jihar Katsina yayin da ake shirin yi masa sutura.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne da kansa zai karɓi gawar, da zarar mataimakinsa, Kashim Shettima da kuma shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila sun sauka a jihar.

An tabbatar da cewa gidan Buhari ya cika da jami’an tsaro a ranar Talata da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), sojojin Najeriya, ’yan sanda, da jami’an tsaron fararen hula (NSCDC).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng