"Da tuni Ya Rasu," An Ji Abin da Ya Ceci Rayuwar Buhari tun Yana Shugaban Ƙasa

"Da tuni Ya Rasu," An Ji Abin da Ya Ceci Rayuwar Buhari tun Yana Shugaban Ƙasa

  • Femi Adesina ya kare matakin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari na zuwa Landan neman lafiya lokacin yana kan mulki
  • Tsohon kakakin shugaban ƙasar ya ce watakila da Buhari ya yi amfani da asibitocin Najeriya a lokacin, da tuni ya rasu
  • Ya ce dole sai yana raye ne zai yi ƙoƙarin gyara harkar lafiyar ƙasar nan, yana mai cewa dama tun kafin ya hau mulki yana zuwa Landan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Femi Adesina, ya ce da Muhammadu Buhari ya dogara da asibitocin Najeriya wajen kula da lafiyarsa, watakila da tuni ya rasu.

Adesina ya ce tsohon shugaban ƙasa ya jima yana zuwa Landan domin a duba lafiyarsa, kuma da ya tsaya a asibitocin Najeriya, mai yiwuwa ba zai kawo.yanzu ba.

Kara karanta wannan

'Masoyin Lagos ne: Tsohon gwamna ya faɗi alherin Buhari bayan rasuwarsa

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Femi Adesina ya kare Buhari kan zuwa Landan neman lafiya Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Adesina ya faɗi haka ne a ranar Talata yayin wani shirin kai tsaye na musamman da Channels Television ta shirya domin girmama marigayi Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa Buhari ke zuwa neman lafiya Landan?

Yayin da yake mayar da martani kan sukar da ake yiwa Buhari saboda yawan zuwa ƙasar Ingila domin jinya lokacin yana kan mulki, Adesina ya kare matakin, yana mai cewa lamari ne na ceton rai.

“Tun kafin ya zama shugaban ƙasa, Buhari yana zuwa gwaje-gwajen lafiyarsa a Landan. Don haka ba lokacin da yake shugaban ƙasa ne kawai ya fara ba, tun tuni yana zuwa can,” in ji Adesina.

Ya bayyana cewa likitocin da ke kula da lafiyar Buhari tun kafin 2015 sun san tarihin lafiyarsa sosai, don haka ba hikima ba ce a sauya su a tsakiyar jinya.

Ya ce ci gaba da jinya a ƙetare ya dogara ne da ƙwarewa da kuma gazawar tsarin kiwon lafiya na Najeriya a wancan lokacin.

Kara karanta wannan

'Darasi 1 da ya kamata shugabannin Najeriya su ɗauka daga rasuwar Shugaba Buhari'

Femi Adesina ya kare Muhammadu Buhari

“Dole sai ya kasance a raye sannan zai gyara wasu abubuwa a ƙasa. Da Buhari ya nace cewa sai an kula da lafiyarsa a nan gida don nuna ƙaunar ƙasa ko wani abu makamancin haka, watakila da tuni ya rasu.

Adesina ya ƙara da cewa rayuwar Buhari da damar da ya samu na shugabantar ƙasa sun dogara da irin kulawar lafiyar da ya samu a ƙasashen waje.

“Dole ne ya rayu tukunna kafin ya iya jagorantar ƙasa zuwa matakin da za a samu irin wannan ƙwarewa ta duba lafiya.
"Don haka waɗanda ke kuka da yawan zuwansa jinya a waje ba su fahimci cewa dole ne mutum ya rayu tukunna kafin ya kawo sauyi ba,” in ji shi.
Buhari tare da Femi Adesina.
Femi Asedina ya ce bai kamata a soki Buhari saboda zuwa neman lafiya a Landan ba Hoto: @FemiAsedina
Source: Twitter

Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa ya ce zaɓin Buhari na kula da lafiyarsa a waje bai kamata a ɗauke shi a matsayin isa ko rashin amincewa da asibitocin cikin gida ba, sai dai ya zama tilas domin ceton rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Mufti Menk ya yi ta'aziyyar Buhari, ya tuna ɗabi'arsa game da Sallah

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa yawan tafiyar Buhari zuwa ƙetare domin jinya ya haifar da cece-kuce, inda mutane da dama ke nuna damuwa kan rashin zama a gida.

Shugabannin ƙasashe 3 za su zo jana'izar Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa ana sa ran shugabannin ƙasashe uku za su halarci jana'izar Muhammadu Buhari a Daura a jihar Katsina.

Shugabannin kasashen Chadi, Gambiya da Guinea Bissau za su iso Daura domin halartar jana’izar tsohon shugaban Najeriya.

Tuni dai Gwamnatin Najeriya ta ayyana hutu a ranar Talata domin bai wa ‘yan Najeriya damar halartar jana’izar Muhammadu Buhari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262