Shugabannin Kasashen Duniya 3 Za Su Hallara Daura Jana'izar Buhari
- Gwamna Dikko Radda na Katsina ya ce Shugaba Bola Tinubu da kansa zai tarbi gawar Muhammadu Buhari a jihar a yau Talata
- Shugabannin kasashen Chadi, Gambiya da Guinea Bissau za su iso Daura domin halartar jana’izar tsohon shugaban Najeriya
- An ayyana Talata a matsayin hutu domin bai wa ‘yan Najeriya dama su halarci jana’izar shugaban daga sassa daban daban
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – A yayin da Najeriya ke shirin jana’izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a Daura, jihar Katsina, Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda ya yi karin haske.
Dikko Radda ya bayyana cewa shugabannin ƙasashen Chadi, Gambiya da Guinea Bissau za su halarci wannan jana’iza mai tarihi.

Source: Facebook
Radda ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar kamar yadda BBC Hausa ta wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce wannan mataki ya nuna irin yadda Buhari ya shahara da mutunci a wajen kasashen ketare.
Gwamnatin Najeriya ta ayyana hutu a ranar Talata domin bai wa ‘yan Najeriya damar halartar jana’izar wanda ya taba shugabantar ƙasar a matsayin soja da kuma mulkin farar hula.
Tinubu da ministoci 25 za su je Daura
Gwamna Radda ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kansa zai tarbi gawar Buhari a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina kafin a wuce da ita zuwa Daura.
Ya ƙara da cewa ministoci 25 daga gwamnatin tarayya za su kwana uku a Daura domin karɓar gaisuwar ta’aziyya a madadin gwamnatin Najeriya.
Gwamnan ya ce:
“Muna sa ran karbar manyan baki da dama daga sassa daban-daban na duniya, ciki har da shugabannin ƙasashen Afrika uku.
“Talakawa daga jihohi daban-daban sun nuna sha’awar zuwa Daura domin halartar jana’izar, shi ya sa gwamnati ta ayyana hutu,”
Shugabannin kasashe da za su je Daura
Shugabannin da ake sa ran za su halarci jana’izar sun haɗa da shugaba Mahamat Idriss Déby Itno na Chadi da ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2024 bayan mulkin rikon kwarya.
Mahamat Idriss Déby Itno ya kasance ɗan tsohon shugaban Chadi, Idriss Déby, wanda ya mulki ƙasar daga 1990 zuwa 2021.

Source: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa shugaba Adama Barrow na Gambiya da ke jagorantar ƙasar tun shekarar 2017 ma zai halarci jana'izar.
Shugaba Umaro Mokhtar Sissoco Embaló na Guinea Bissau da ya fara shugabanci tun 2020 na cikin manyan shugabannin da za su halarci jana'izar shugaba Buhari.
Jana’izar za ta gudana ne a gidansa da ke Daura da misalin ƙarfe 2:00 na rana a yau Talata, bayan isowar gawarsa daga London da misalin ƙarfe 12:00 na rana.
Gawar Buhari ta taho daga London
A wani rahoton, kun ji cewa, gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa Kashim Shettima ya dauko gawar Buhari daga London.
Mataimakin shugaban kasar ya tashi daga Najeriya zuwa London domin tahowa da gawar tun bayan rasuwar shugaba Buhari.
Tawagar mataimakin shugaban kasar ta hada da manyan jami'an gwamnatin tarayya da gwamna Babagana Zulum.
Asali: Legit.ng


