An Gano Bidiyon Aisha Buhari Tana Rusa Kuka a gaban Shettima yayin da Ya Ke Ta'aziyya
- Ana cigaba da jimami bayan mutuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a birnin London a ranar Lahadi
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yana daga cikin wadanda suka je London domin dauko gawar marigayin wanda a yanzu an ce suna kan hanya
- An gano matar tsohon shugaban kasa, Aisha Buhari a cikin wani bidiyo tana hawaye yayin ziyarar ta’aziyyar Kashim a London
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa an dauko gawar marigayi Muhammadu Buhari daga birnin London.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shi ne ya jagoranci rakiyar dawowa Najeriya da gawar a yau Talata 15 ga watan Yulin 2025.

Source: Twitter
Channels TV ta wallafa wani faifan bidiyo da aka gano Aisha Buhari na zubar da hawaye yayin ta'aziyyar Shettima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da Tinubi ya yi bayan rasuwar Buhari
Bola Tinubu ya aika mataimakinsa, Kashim Shettima da sakon ta'aziyya ga iyalan Buhari, wanda suka karɓi bakuncin ziyarar a birnin London bayan rasuwar tsohon shugaban.
Femi Gbajabiamila da Yusuf Maitama Tuggar sun raka Shettima zuwa gidan iyalan Buhari a matsayin tawagar ta'aziyya daga shugaban kasa Tinubu.
Tinubu ya ba da umarni cewa a daga tutocin kasa kasa-kasa na tsawon kwanaki bakwai daga Lahadi, 13 ga Yuli, ranar rasuwar Buhari domin mutunta shi.

Source: Twitter
Tinubu ya jajantawa iyalan Buhari bayan rasuwarsa
Gwamnatin tarayya ta aike da ta'aziyya ga iyalansa, mutanen jihar Katsina da ‘yan Najeriya gaba ɗaya, tana masa addu’a don samun rahamar Allah.
Har ila yau, Tinubu ya ayyana yau Talata 15 ga watan Yulin 2025 a matsayin ranar hutu a fadin Nigeria baki daya domin jimamim mutuwar Buhari.
Wasu 'yan siyasa da suka hada da Goodluck Jonathan da Atiku Abubakar da sauransu sun aike da sakon ta'aziyya, suna cewa rasuwar Buhari babban rashi ne.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Cikin hawaye, Fatima Buhari ta isa Daura inda za a binne gawar mahaifinta
Marigayi Buhari na daga cikin fitattun shugabannin siyasar Najeriya, wanda wasu ke kallonsa da tsantsar kishin kasa a zuciyarsa.
Bidiyon Aisha Buhari cikin jimami a London
An bayyana matar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta tana kuka sosai bayan rasuwar mijinta a ranar Lahadi, 13 ga Yuli.
An ga tsohuwar uwargidan marigayin cikin bidiyo tana kuka yayin ziyarar ta’aziyyar shugaban kasa ga iyalan Buhari a London ranar Litinin, 14 ga Yuli.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, Femi Gbajabiamila da Yusuf Tuggar sun jagoranci ziyarar domin isar da sakon Tinubu ga iyalan Buhari.
Aisha Buhari, tsohuwar uwargida kuma matar Buhari wanda ya rasu a wani asibiti a London ranar Lahadi, ta bayyana cikin wani irin yanayi mai taba zuciya.
An ga Aisha Buhari cikin bakaken kaya da wasu daga cikin iyalanta tana kuka yayin ziyarar Shettima ga iyalan tsohon shugaban kasa a London bisa umarnin Tinubu.
Buba Galadima ya yi jimamin mutuwar Buhari
Kun ji cewa tsohon abokin Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya bayyana alhini kan rasuwar tsohon shugaban kasar Najeriya.
An ce Buba Galadima ya yafewa marigayin duk da irin sukar gwamnatinsa da ya a wancan lokaci daga 2015 zuwa shekarar 2023.
Har ila yau Buba Galadima ya ce ya karɓi sakonni daga mutane da dama da ke taya shi alhinin rasuwar tsohon abokinsa.
Asali: Legit.ng

