'Ya Yiwa Yan Najeriya Iya Kokarinsa,' Abin da Abdulsalami Ya ce kan Buhari
- Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Janar AbdulSalami Abubakar mai ritaya ya bayyana kaduwa da samun labarin rasuwar Muhammadu Buhari
- Ya bayyana cewa sun yi jinya tare da tsohon shugaban kasa a asibiti daya da ke birnin Landan kafin a sallame shi bayan ya samu sauki sosai
- Daga cikin halayen Buhari da ya bayyana, AbdulSalami ya ce marigayin yana da rikon amana da kokarin ciyar da Najeriya gaba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya ce sun yi jinya tare, a asibitin daya da marigayi Muhammadu Buhari, a birnin Landan kafin rasuwarsa.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi yana da shekaru 82, bayan doguwar jinya da ba a bayyana cutar ba.

Source: Getty Images
A wata hira da aka yi da shi a Channels TV, Abdulsalami ya ce ya samu labarin rasuwar Buhari ne jim kadan bayan da aka sallame shi daga asibitin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdulsalami ya bayyana halayen Buhari
Arise News ta ruwaito cewa, yayin da yake tunawa da dangantakar su da ta kai kusan shekaru 60, Abdulsalami ya ce sun hadu da Buhari a shekarar 1962, lokacin da suka shiga rundunar sojin Najeriya tare.
Tsohon shugaban mulkin soja ya ce:
"Shi ne babba a wurina; kuma lokacin yakin basasa, muna cikin tsagi guda da shi."
Ya bayyana Buhari a matsayin mutum mai nutsuwa da gaskiya, tare da bayar da tabbacin cewa ba za taba cin amanar da aka ba shi ba.
Ya kara da cewa:
"Za ka iya dora wa Buhari duk wani abu a doron duniya, ba zai cutar da kai ba."
Abdulsalami: ‘Buhari ya yi iya kokarinsa’
Game da mulkin Buhari a matsayin shugaban kasa a tsarin dimokradiyya, Abdulsalami ya yaba da kokarinsa na yaki da cin hanci da rashawa.

Source: Facebook
Sai dai ya amince cewa wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa ba su cika alkawarin da Buharu ta dora masu ba.
Ya ce:
“Lokacin da ya zama shugaban kasa na dimokradiyya, ya yi iya kokarinsa wajen yakar rashawa. Amma abin takaici, wasu daga cikin wadanda suka yi aiki tare da shi ba su sauke nauyin da aka dora masu ba."
Abdulsalami ya bayyana cewa rasuwar Buhari babban gibi ne ga Najeriya da ma yankin Afrika baki daya.
An samu bayanai kan rasuwar Buhari
A baya, kun ji cewa rahotanni sun fara bayyana dangane da yadda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kwana a Landan kafin rasuwarsa a ranar Lahadi.
Makusancinsa, Mamman Daura ya bayyana cewa sun yi hira a cikin nishadi da tsohon shugaban, yayin da ake shirin sallamarsa a ranar Lahadi domin ya dawo gida Najeriya.
Sai dai cikin ikon Allah, an ruwaito cewa jikin tsohon shugaban ya rikice da karin kumallo, inda daga nan ne kuma jikin bai yi dadi ba har ya koma ga Mahalicci da 4.30 na yamma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

