Buhari: Jerin Shugabannin da Najeriya Ta Rasa Tun 'Yancin Kai
FCT, Abuja - Tun bayan samun ƴancin kai, Najeriya ta rasa wasu daga cikin shugabannin da suka jagoranceta.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Wasu daga cikin waɗannan shugabannin dai sun rasu ne sakamakon ciwo ko rashin lafiya, yayin da wasu kuma kashe su aka yi.

Source: Twitter
Shugabannin Najeriya da suka rasu
Shugaba na baya-bayan nan da ya rasu shi ne, Muhammadu Buhari wanda ya rasu a birnin Landan, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai shugabannin Najeriya guda takwas da suka riga mu gidan gaskiya tun bayan samun ƴancin kai.
Ga jerinsu a nan ƙasa:
1. Abubakar Tafawa Balewa
Abubakar Tafawa Balewa shi ne Firaminista na farko a Najeriya bayan samun ƴancin kai.
Ya yi wa’adin mulki daga shekarar 1957 zuwa 1966, lokacin da aka yi juyin mulki na farko a Najeriya, inda aka sace shi sannan aka kashe shi.
A lokacin mulkinsa, Abubakar Tafawa Balewa ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa ƙungiyar haɗin kan Afirka (OAU), kuma ya yi kakkausar suka kan kisan gillar Sharpeville da ya faru a Afirka ta Kudu.
2. Jonathan Aguiyi Ironsi
J.T.U Aguiyi Ironsi shi ne shugaban soja na farko a Najeriya, bayan kifar da gwamnatin farar hula ƙarƙashin Tafawa Balewa a ranar 15 ga Janairu, 1966.
Bayan wata shida da hawa mulki, an kifar da shi a wani juyin mulki na ramuwar gayya a ranar 29 ga Yuli, 1966.
An kashe shi ne ta hannun wasu sojoji daga Arewacin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Murtala Mohammed.
Yayin wata hira da jaridar Daily Trust, dogarinsa Sani Bello, ya bayyana cewa an kai tsohon shugaban ne cikin daji sannan aka harbe shi.
3. Murtala Mohammed
Murtala Mohammed ya rasu yana da shekaru 37, tare da dogarinsa, Laftanar Akintunde Akinsehinwa, a cikin motarsa baƙar Mercedes Benz a ranar 13 ga Fabrairu, 1976.
Motarsa ta faɗa tarko ne a hanyarsa ta zuwa ofishinsa da ke Dodan Barracks, Legas.
Janar Murtala Muhammad ya hau mulki a ranar 29 ga Yuli, 1975 bayan kifar da Janar Yakubu Gowon, wanda a lokacin yake halartar taron kolin OAU a birnin Kampala na ƙasar Uganda.

Kara karanta wannan
Shin ya kamata ƴan Najeriya su yafewa Buhari? Sheikh Aminu Daurawa ya roƙi abubuwa 2
4. Sani Abacha
A ranar Litinin, 8 ga Yuni, 1998, Sani Abacha ya rasu a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock, da ke Abuja.
An binne shi a ranar da ya mutu bisa ƙa’idar Musulunci, ba tare da an yi masa binciken gawa ba, lamarin da ya haifar da jita-jita cewa wataƙila guba aka sanya masa.
Bayan rasuwarsa, Janar Abdulsalami Abubakar ya zama shugaban ƙasa, inda bai daɗe ba ya miƙa mulki a hannun farar hula.
5. Umaru Musa Yar’adua

Source: UGC
Umaru Musa Yar’adua ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa daga 2007 zuwa watan Mayun 2010, lokacin da ya rasu.
Ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 21 ga watan Afrilu, 2007, kuma aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, 2007.
Kafin rasuwarsa, Umaru Musa Yar'adua ya yi fama da rashin lafiya a kasashen Saudi da Jamus.
6. Shehu Shagari

Source: Twitter
Tsohon shugaban ƙasa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari ya rasu a ranar Juma’a, 28 ga watan Disamba 2018.
Ya rasu a asibitin ƙasa da ke Abuja, yana da shekaru 93. An haife shi a ranar 25 ga Fabrairu, 1925.
Shehu Shagari ya yi shugabancin Najeriya a Jamhuriya ta biyu (1979–1983), bayan da Janar Olusegun Obasanjo ya miƙa mulki ga farar hula.
7. Ernest Shonekan

Source: UGC
Chief Ernest Shonekan, wanda ya shugabanci gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasa da ta biyo bayan gwamnatin soja ta Janar Ibrahim Babangida, ya rasu a safiyar ranar Talata.
Ya rasu a Legas, yana da shekaru 85, a asibitin Evercare, Lekki, bayan doguwar rashin lafiya. Majiyoyi sun ce an kwantar da shi a asibiti fiye da wata biyu kafin rasuwarsa.
Ya shugabanci Najeriya daga 26 ga Agusta zuwa 17 ga Nuwamba, 1993, kafin a kifar da shi ta hanyar juyin mulki ƙarƙashin marigayi Janar Sani Abacha.
Jaridar Daily Trust ta ce iyalansa sun tabbatar da rasuwarsa tare da cewa ya rasu ne sakamakon rashin lafiya.
8. Muhammadu Buhari

Source: Facebook
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025 a wani asibiti da ke birnin Landan.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Ganin karshe da 'yan Najeriya suka yi wa Buhari, yana tare da Atiku, El-Rufai
Mai magana da yawun bakinsa, Garba Shehu, ya tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa da.ya fitar a shafin X.
Muhammadu Buhari ya rasu ne bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya wacce ba a bayyana kowace iri ba ce.
Gwamnati ta ba da hutu saboda rasuwar Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu saboda rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Gwamnatin ta ayyana ranar Talata, 15 ga watan Yulin 2025 a matsayin ranar da babu aiki don karrama tsohon shugaban ƙasan.
Muhammadu Buhari dai ya yi bankwana da duniya ne bayan ya yi jinyar rashin lafiya a wani asibiti da ke birnin Landan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

