Mamman Daura: Bayanai Sun Fara Fito wa kan Rasuwar Muhammadu Buhari

Mamman Daura: Bayanai Sun Fara Fito wa kan Rasuwar Muhammadu Buhari

  • Makusancin tsohon shugaban kasa, Mamman Daura ya bayyana yadda ya rabu da Muhammadu Buhari kafin rasuwarsa
  • Ya ce sun gana a cikin nishadi da Buhari a ranar Asabar, inda aka fara shirye-shiryen sallamo shi daga asibiti da ke Landan zuwa gida
  • Mamman Daura, ya kara da bayyana cewa sai dai a ranar Lahadi, da karin kumallo ne aka gano jikin Buhari ya yi tsanani sosai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Sababbin bayanai sun bayyana a ranar Litinin dangane da yadda tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya kwana kafin rasuwarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa yana tare da daya daga cikin amintattunsa kuma dan uwansa na jini, Mamman Daura, da kuma wasu 'yan uwa na kusa da shi.

Kara karanta wannan

'Akwai alaƙa mai kyau tsakaninsu': Bidiyon haɗuwar Buhari da Tinubu na ƙarshe

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Mamman Daura ya yi bayanin rabuwarsa da Buhari Hoto: @MBuhari
Source: Facebook

A wata hira da ta kebanta da jaridar ThisDay, Mamman Daura ya bayyana cewa yana tare da marigayi shugaban kasa a ranar Asabar, kafin rasuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an fara shirye-shiryen sallamar Buhari daga asibiti a karshen makon nan, kafin lafiyarsa ta rikice a ranar Lahadi.

Rashin lafiyar Buhari ta tsananta

Arise News ta wallafa cewa wasu daga cikin 'yan uwa da suka yi magana sun ce babu wani alamar da ke nuna cewa tsohon shugaban kasar ba zai tsira daga wannan rashin lafiya ba.

Mamman Daura ya kara da cewa an riga an fara tsara yadda za a biya kudin otal na dukkannin wadanda ke tare da Buhari a birnin Landan kafin sallamarsa daga asibiti.

Ya ce ya bar Muhammadu Buhari ne cikin nishadi a ranar Asabar, yana fatan komawa ganin sa a ranar Lahadi.

Ya ce:

“Mun kasance tare da shi a ranar Asabar muna hira da dariya kuma yana cikin nishadi a asibitin Landan da aka kwantar da shi. Mun tattauna abubuwa da dama. Har ma yana da shirin komawa Najeriya bayan sallamarsa daga asibiti a wannan makon."

Kara karanta wannan

'Abin duniya na banza ne,' Wasu daga cikin shawarwarin Buhari ga ƴan Najeriya

Buhari ya rasu a Landan

Sai dai rahotanni sun ce lafiyar Buhari ta tsananta a ranar Lahadi yayin karin kumallo, inda ya fara fama da matsalar numfashi da misalin 12.00 na rana.

Yadda Buhari ya rasu a Landan
Mamman Daura ya ce Buhari ya rasu a ranar Lahadi Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Likitoci da ke bakin aiki sun yi iya kokarinsu wajen ceto rayuwarsa, amma daga bisani ya rasu da misalin 4.30 na yammacin ranar.

Daura ya ce:

“Na bar shi da misalin 9.00 na dare a ranar Asabar yana cikin nishadi, kuma na yi masa alkawarin zan dawo na gan shi da rana a ranar Lahadi. Yana sa ran ganin likitansa da safe, amma da rana sai matsalar numfashi ta fara samun matsala, likitoci suka ruga don ceto shi. Abin takaici, da misalin karfe 4:30 na yamma, ya rasu.”

Mufti Menk ya yiwa Buhari addu'a

A baya, mun wallafa cewa fitaccen malamin addinin Musulunci daga kasar Zimbabwe, Sheikh Mufti Ismail Menk, ya bayyana alhinin rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Rasuwar Buhari ta taɓa Ndume, ya faɗi wasu abubuwa da ya sani

Mufti Menk ya shiga cikin jerin mashahuran malamai da shugabanni na duniya da ke aiko da sakon ta’aziyya ga ‘yan Najeriya da iyalan marigayi Buhari da ya rasu a ranar Lahadi.

Ya a bayyana Muhammadu Buhari a matsayin shugaba nagari, wanda ya kasance mai tsoron Allah, da rikon amana a rayuwarsa ta shugabanci tare da kokarin tsayar da Sallah.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng