Gwamnonin Arewa 7 Sun Haɗa Baki, Sun ba da Hutun Kwana 1 saboda Rasuwar Buhari

Gwamnonin Arewa 7 Sun Haɗa Baki, Sun ba da Hutun Kwana 1 saboda Rasuwar Buhari

  • Kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma ta ba da hutun kwana guda a jihohin yankin bakwai domin girmama Muhammadu Buhari
  • A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Katsina ya fitar, ta ce rasuwar Buhari babban rashi ne ga ƙasa baki ɗaya
  • Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya rasu ne bayan jinyar makonni a wani asibiti a birnin Landan na ƙasar Birtaniya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Gwamnonin Arewa maso Yamma sun ayyana ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, a matsayin ranar hutu na musamman a duka jihohin bakwai na yankin

Gwamnonin sun ba da wannan hutu ne domin girmamawa ga marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu ranar Lahadi a wani asibiti a Birtaniya.

An ba da hutu a jihohi 7 saboda rasuwar Buhari.
Gwamnonin Arewa maso Yamma sun ayyana hutun gobe Talata domin karrama Buhari Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya rattaba wa hannu, wanda kakakinsa ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu saboda rasuwar Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni 7 sun kaɗu da rasuwar Buhari

Gwamnonin sun bayyana alhini da baƙin ciki matuƙa kan rasuwar tsohon shugaban ƙasa, suna cewa rasuwarsa babban rashi ne ga Najeriya.

“Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma ta kaɗu da labarin rasuwar tsohon shugaban ƙasarmu, Janar Muhammadu Buhari. Ya rasu ne jiya a wani asibiti da ke Birtaniya,” in ji sanarwar.

Gwamna Radda ya yaba wa Buhari a matsayin “uba, jagora kuma abin alfahari ga yankin Arewa maso Yamma,” yana mai cewa rayuwarsa cike take da sadaukarwa, gaskiya da amana.

Jihohin Arewa 7 da aka bada hutun gobe

Don girmamawa, gwamnonin sun amince da ayyana ranar Talata a matsayin hutu a jihohin Kaduna, Katsina, Kano, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara domin bai wa jama’a damar alhinin wannan rashi.

“Wannan mataki yana nuna girmamawa da darajar da muka ba mutumim da ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya domin hidima ga Najeriya,” in ji Radda.

Kara karanta wannan

Shin ya kamata ƴan Najeriya su yafewa Buhari? Sheikh Aminu Daurawa ya roƙi abubuwa 2

Sanarwar ta ƙara da cewa za a kawo gawar marigayin tsohon shugaban ƙasa zuwa garinsa na haihuwa, wato Katsina, da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Talata.

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Gwamnoni sun roki ƴan Najeriya su sanya Buhari a addu'a Hoto: @MBuhari
Source: Getty Images

Gwamnoni sun roki ƴan Najeriya alfarma

Kungiyar gwamnonin ta yi kira ga ‘yan Najeriya daga kowane ɓangare su yi wa Buhari addu'ar samun gafara da rahamar Allah SWT.

Radda ya miƙa ta’aziyya a madadin kungiyar ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, iyalan mamacin, gwamnatin da al’ummar Jihar Katsina, da dukan ‘yan Najeriya da ke alhinin rasuwar wannan dattijo.

“Allah (SWT) ya jikansa Ya sanya shi Aljannatul Firdaus, ya kuma ba iyalansa, abokansa da dukan ƴan ƙasa haƙurin jure wannan babban rashi,” in ji shi.

Sheikh Daurawa ya roƙi a yafewa Buhari

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya roki al'ummar Najeriya su yi wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari addu'ar samun rahama.

Babban kwamandan Hisbah na Kano ya kuma roki ƴan Najeriya da su yafe wa Buhari idan ya masu laifi a tsawon lokacin da ya shafe a kan mulkin Najeriya.

Tun bayan sanar da rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Buhari, ƴan Najeriya suka fara alhini tare da bayyana ra'ayoyinsu kan halin da aka shiga a shekaru takwas na mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262