Shin Ya Kamata Ƴan Najeriya Su Yafewa Buhari? Sheikh Aminu Daurawa Ya Roƙi Abubuwa 2

Shin Ya Kamata Ƴan Najeriya Su Yafewa Buhari? Sheikh Aminu Daurawa Ya Roƙi Abubuwa 2

  • Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya roki ƴan Najeriya su sanya Muhammadu Buhari a addu'o'insu kana su yafe masa kura-kuransa
  • Babban kwamandan rundunar Hisbah ta Kano ya yi wannan roko ne yayin da ake jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasar a Najeriya
  • A ranar Lahadi da ta gabata ne Allah ya karɓi ran Buhari, waɓda ya shafe shekaru takwas yana mulkin Najeriya daga 2015 zuwa 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Fitaccen malamin addinin musulunci kuma babban kwamandan Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya roƙi ƴan Najeriya su yafe wa Muhammadu Buhari.

Tun bayan sanar da rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Buhari, galibin ƴan Najeriya suka fara alhini tare da bayyana ra'ayoyinsu kan halin da aka shiga a shekaru takwas na mulkinsa.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da marigayi Muhammadu Buhari.
Daurawa ya roki ƴan Najeriya su yafewa Shugaba Buhari Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Sheikh Daurawa ƴa roki a yafewa Buhari

Kara karanta wannan

'Darasi 1 da ya kamata shugabannin Najeriya su ɗauka daga rasuwar Shugaba Buhari'

Amma a wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Aminu Daurawa ya roƙi ƴan Najeriya su yafewa Marigayi Buhari kura-kuran da wataƙila ya aikata masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya kuma roƙi jama'a su yiwa tsohon shugaban ƙasar addu'ar samun rahama a wurin Allah bayan rasuwarsa a birnin Landan.

A gajerren saƙon, Sheikh Daurawa ya ce:

Ina raƙonmu, mu yiwa Baba Buhari Addu'a, kuma mu yafe masa."

Ƴan Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan yafewa Buhari laifin da wataƙila ya aikata lokacin da yake shugabancin Najeriya.

Wasu ƴan Najeirya sun yafewa Buhari

Kwamared Umar Idris Dabai ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa shi a karan kansa, ya yafewa Buhari duk wani haƙƙinsa da ke kansa.

Umar ya ce duk da mutane da yawa na ganin Buhari ya ba su kunya bayan sun sha wahala sun zaɓe shi a 2015, amma kuma sun ji raɗaɗin rasuwarsa.

A cewarsa, shi kansa ya ji ba daɗi da ya samu labarin rasuwar Muhammadu Buhari, yana mai cewa ya yafe masa duniya da lahira.

"Mutum ajizi ne, ni a karan kaina, idan ma akwai wani laifi da Buhari ya mani a lokacin mulkinsa, wallahi na yafe masa duniya da lahira, Allah Ya jiƙansa ya gafarta masa," in ji Umar.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 7 su haɗa baki, sun ba da hutun kwana 1 saboda rasuwar Buhari

Muhammadu Buhari.
Wasu ƴan Najeriya sun sanar da yafewa Marigayi Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: UGC

Shin ya kamata a riƙa zagin Buhari?

Haka nan wata mata, Umma Sulaiman ta bi sahun Kwamared Umar wajen yafewa Buhari.

A cewarta, duk da an sha wahala a mulkinsa mai yiwuwa ba shi da laifin komai amma mutane ke ta zaginsa.

"Ba na jin daɗin yadda wasu ke zagin Buhari tun ba yau ba, za ta iya yuwuwa ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen sauke nauyin jama'a, yanzu su masu zaginsa suna tunanin Allah ba zai tambaye su ba ne?
"Ni na yafe wa Buhari tun yana raye idan ma ya yi laifin kenan, ina fatan Allah Ya gafarta mana baki ɗaya," in ji ta.

An ɗage jana'izar Muhammadu Buhari

A wani labarin, kun ji cewa an ɗage jana'izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari Buhari zuwa ranar Talata, 15 ga watan Yuli, 2025.

Buhari, wanda ya rasu a wani asibiti a Landan bayan jinya makonni, za a dawo da shi mahaifarsa Daura domin yi masa sutura.

Tuni dai tawagar gwamnatin tarayya karƙashin jagorancin, Kashim Shettima ta isa Landan domin dawo da gawar Buhari zuwa gida Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262