Rasuwar Buhari: Matakin da APC Ta Dauka don Karrama Tsohon Shugaban Kasa

Rasuwar Buhari: Matakin da APC Ta Dauka don Karrama Tsohon Shugaban Kasa

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bi sahun masu alhini kan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya rasu a birnin Landan
  • Domin karrama tsohon shugaban ƙasan, APC ta sanar da rufe hedkwatarta ta ƙasa daga ranar Litinin, 14 ga watan Yulin 2025
  • Wannan matakin dai na zuwa ne yayin da ake jiran isowar gawar Buhari daga birnin Landan na ƙasar Birtaniya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta yi jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari.

Jam'iyyar APC ta sanar da rufe hedikwatarta ta ƙasa da ke Abuja a matsayin girmamawa ga marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

APC ta yi alhinin rasuwar Buhari
APC ta kulle hedkwatarta kan rasuwar Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC na ƙasa, Barrista Felix Morka, ya fitar a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Mun yi babban rashi,' Ganduje ya mika ta'aziyya ga 'yan Najeriya kan rasuwar Buhari

Buhari ya rasu bayan rashin lafiya

Buhari ya rasu a birnin Landan a jiya Lahadi bayan fama da wata doguwar rashin lafiya da ba a bayyana ba.

An dai shirya binne tsohon shugaban ƙasan na Najeriya a yau (Litinin) a garinsa na Daura da ke jihar Katsina.

Ana sa ran shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sauran tsofaffin shugabannin Najeriya za su halarci jana'izar Buhari.

Tuni dai Shugaba Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima da yaje birnin Landan domin yi wa gawar Buhari rakiya zuwa gida Najeriya.

APC ta rufe hedkwatarta saboda Buhari

APC ta ce za a rufe hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa daga yau Litinin kuma za a buɗe ta a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuli, 2025.

"Bisa umarnin muƙaddashin shugaban jam’iyyarmu mai girma, Hon. Bukar Dalori, za a rufe hedikwatar jam’iyyar daga yau, Litinin 14 ga watan Yuli, kuma za a buɗe ta ranar Alhamis, 17 ga watan Yuli, 2025.”

Kara karanta wannan

El Rufai ya yi alhinin rasuwar Buhari, ya fadi halascin da ya yi masa

“Muna ƙarfafa gwiwar mambobin jam’iyya da su yi amfani da wannan lokacin na jimamin ƙasa wajen yin tunani cikin natsuwa da kuma addu’a domin samun rahama ga ruhin wannan jagora da ya riga mu gidan gaskiya."

- Felix Morka

APC ta karrama Muhammadu Buhari
APC ta yi jimamin rasuwar Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Twitter

Karanta wasu labaran kan rasuwar Buhari

El-Rufai ya yi ta'aziyyar Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi ta'aziyya kan rasuwar Muhammadu Buhari.

Nasir El-Rufai ya bayyana tsohon shugaban ƙasan a matsayin wanda ya hidimtawa Najeriya a lokacin yaƙi da zaman lafiya.

Ya yaba masa kan irin gudunmawar da ya ba shi a siyasance, tare da ƙarfafa masa gwiwa ya tsaya takarar gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng