An Dage Jana'izar Marigayi Shugaba Buhari, an Saka Sabon Lokaci
- Ana shirin kawo gawar marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga London zuwa Najeriya domin jana’iza
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umurci Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da ya jagoranci dawowar gawar daga London
- ’Yan Najeriya na ci gaba da jimami da alhini sakamakon rasuwar shugaban da ya jagoranci Najeriya a har sau biyu a mulkin dimokuradiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayan rasuwarsa a asibitin London a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, ana shirin kawo gawar marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari Najeriya a gobe Talata
Rahotanni sun tabbatar da cewa za a dauko gawar ne domin jana’iza a garinsa na Daura, jihar Katsina.

Source: Facebook
Shugaban karamar hukumar Katsina, Isah Miqdad ya wallafa a X cewa sai gobe Talata da misalin karfe 12:00 na rana gawar za ta iso Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga haka, Hon. Isah Miqdad ya ce za a yi wa Buhari jana'iza a karamar hukumar Daura da misalin karfe 02:00 na rana kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Hakan ya saba da bayanan da aka samu a karon farko cewa za a yi wa marigayin jana'iza a yau Litinin.
Shettima ya jagoranci dauko gawar Buhari
Da yake magana jim kadan bayan isa London, Kashim Shettima ya tabbatar da cewa ya zo ne bisa umarnin shugaban kasa Bola Tinubu domin jagorantar dawo da gawar marigayi Buhari.
A wata sanarwa da ofishin mataimakin shugaban kasa ya wallafa, an ce:
“Mataimakin shugaban kasa, tare da shugaban ma’aikata Femi Gbajabiamila, ya isa London kuma aka tarbe su da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno.”
“Shettima ya sauka London ne bisa umarnin shugaban kasa domin raka gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa Najeriya domin jana’iza a Daura, jihar Katsina.”

Source: Twitter
Jimami na ci gaba da karade Najeriya
Tuni al’umma daga sassa daban-daban na Najeriya ke ci gaba da bayyana alhini da jimami sakamakon rasuwar shugaban da suka ce ya nuna kishi da gaskiya a lokacin mulkinsa.
A Daura, garin da Buhari ya fito, mutane na ci gaba da taruwa a unguwanni domin yi masa addu’a tare da jajanta wa iyalansa da danginsa.
Za a yi jana’izar Buhari a Daura
Tuni aka fara shiryawa jana’izar Buhari da za a gudanar a Daura, inda aka shirya gabatar da sallar jana’iza a gobe talata bayan dage ta daga Litinin.
Ana sa ran shugabannin siyasa, na addini da na gargajiya daga fadin kasar za su halarci jana’izar domin girmama marigayin.
IBB ya yi ta'aziyyar shugaba Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya nuna damuwa kan rasuwar Muhammadu Buhari.
Janar Babangida ya bayyana cewa ya fara haduwa da Muhammadu Buhari ne a shekarar 1962 a gidan soja.
Babangida ya tura sakon jaje ga Aisha Muhammadu Buhari tare da rokon Allah ya gafarta wa mijinta, ya sanya shi a aljanna.
Asali: Legit.ng

