Abin da Shugabannin Kasashen Duniya ke Cewa game da Buhari bayan Allah Ya Masa Rasuwa

Abin da Shugabannin Kasashen Duniya ke Cewa game da Buhari bayan Allah Ya Masa Rasuwa

Ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan, bayan ya shafe makonni ana jinyarsa.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Buhari ya shugabanci Najeriya a matsayin shugaban ƙasa na farar hula daga 2015 zuwa 2023, bayan ya mulki ƙasar a matsayin soja daga Janairu 1984 zuwa Agusta 1985.

Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.
Ana ci gaba da aiko sakon ta'aziyyar Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Twitter

Tsohon kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu ya sanar da rasuwar Buhari a shafinsa na X da yammacin ranar Lahadi.

Buhari ya sha fama da rashin lafiya

A lokacin mulkinsa, Buhari ya kasance yana yawan zuwa ƙasar Birtaniya don neman lafiya, an ce ya samu sauƙi sosai bayan barin mulki a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai jikinsa ya sake motsawa a watan Afrilu 2025, lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibiti a Ingila, inda ya shafe makonni yana jinya.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Yadda aka binne gawar Muhammadu Buhari a Daura

Tun bayan da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya sanar da rasuwarsa, ana ci gaba da aika saƙonnin ta’aziyya daga ciki da wajen Najeriya.

Shugabannin ƙasashen duniya sun bayyana alhini da ta’aziyya dangane da rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Legit Hausa ta tattaro maku jerin shigabannin ƙasashe 10 n duniya da suka yi alhinim rasuwar Buhari.

1. Shugaban Saliyo, Julius Maada Bio

Shugaban ƙasar Saliyo kuma shugaban kungiyar ƙasashen Yammacin Afirka watau ECOWAS na yanzu, Julius Maada Bio, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Buhari.

Julius Maada Bio ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan Buhari, gwamnatin Najeriya da sauran ƴan ƙasa a wani sako da ya wallafa a X.

"A madadin al’ummar Saliyo, ina miƙa ta’aziyyarmu ga iyalinsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da kuma al’ummar Najeriya a wannan lokaci mai matuƙar wahala.
“Wannan babban rashi ne ƙwarai, kuma zuciyarmu tana tare da ku duka," in shi.

2. Firaministan Habasha ya yi ta'aziyyar Buhari

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed Ali, ya miƙa ta’aziyyarsa tare da nuna goyon bayansa ga Najeriya a lokacin wannan juyayi na kasa.

Kara karanta wannan

"Da tuni ya rasu," An ji abin da ya ceci rayuwar Buhari tun yana shugaban kasa

Ahmed ya bayyana Buhari a matsayin mutumin kirki wanda ya yi wa ƙasarsa hidima, yana mai miƙa ta'aziyya ga iyalai da gwamnatin Najeriya.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Ahmed Ali ya ce:

A madadin gwamnati da al’ummar Habasha, ina miƙa ta’aziyyar ga iyalan tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, da Gwamnatin Najeriya. Zuciyarmu na tare da ku a wannan lokaci na jimami."

3. Firaministan Indiya ya kaɗu da rasuwar Buhari

Firaminista Ƙasar Indiya, Narendra Modi ya miƙa sakon ta'aziyyar rasuwar Buhari madadin ɗaukacin al'ummarsa.

A wani saƙo da ya wallafa a X ranar Litinin, Modi ya yaba da hikima da jajircewar marigayi Buhari wajen ƙarfafa dangantakar Indiya da Najeriya a lokacin mulkinsa na shekaru takwas.

“Na yi matuƙar bakin ciki da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa na Najeriya, Muhammadu Buhari. Na tuna da ganawa da tattaunawarmu a lokuta da dama.
Hikimarsa, halayensa da jajircewarsa wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin Indiya da Najeriya suna bani sha'awa. A madadin mutane biliyan 1.4 na Indiya muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, al’ummar Najeriya da Gwamnati.”

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 7 su haɗa baki, sun ba da hutun kwana 1 saboda rasuwar Buhari

- In ji Narendra Modi.

4. Sarkin Moroko ya yi ta'aziyyar Buhari

Mai Martaba Sarki Mohammed VI na ƙasar Maroko ya aike da saƙon ta’aziyya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da al’ummar Najeriya bisa rasuwar Muhammadu Buhari.

A cikin saƙon da aka aiko daga birnin Rabat ranar Litinin, Sarkin Maroko ya bayyana jimamin rasuwar Buhari, yana mai bayyana shi a matsayin “jajirtacce” wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa ƙasarsa hidima.

“Ina cikin bakin ciki tare da ku, kuma ina so ku sani cewa na yi matuƙar godiya da hadin kai da zaman aiki da na yi da marigayi,” in ji Sarki Mohammed VI.

Tsohon kakakin shugaban ƙasa, Garba Shehu ya wallafa wannan saƙon ta'aziyya a shafinsa na X.

Sarkin Moroko ya yi ta'aziyyar Buhari.
Sarkin kasar Moroko ya tuna wasu daga cikin halayen Muhammadu Buhari Hoto: @GarShehu
Source: Twitter

5. Shugaban Cote d'Ivoire, Alaassane Ouattara

Shugaban ƙasar Cote d'Ivoire, Alaassane Ouattara shi ma ya bi sahu wajen aika ta'aziyyar ruwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Ya ce ya yi bakin cikin rasuwar Buhari, wanda ya bayyana da mutumin kirki da ya yi ƙoƙarin haɗa kan Najeriya, Cote d'Ivoire da sauran kasashen Afrika.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu saboda rasuwar Buhari

A shafinsa na Facebook, Shugaba Ouattara ya ce:

"Na yi baƙin cikin rasuwar ɗan uwana tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. Marigayin ya taimaka wajen haɓaka danganta tsakanin Najeriya da Cote d'Ivoire.

6. Shugaba Ramaphosa na Afirka ta Kudu

A nasa sakon ta'aziyyar, Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta kudu ya tuna yadda Buhari ya jajirce wajen haɗa kan ƙasashen Afirka.

Ya ce:

"Mu a Afirka ta Kudu muna tare da Najeriya a lokacin da take cikin matuƙar jimami bisa wannan rashi. Mulkin Buhari ya ƙara danƙon zumunci tsakanin ƙasashenmu."

7. Shugaban Kenya ya yi alhinin rasuwar Buhari

Shugaba William Ruto ya nuna alhinin rasuwar Muhammadu Buhari, yana mai cewa wannan rashi ne ga Afirka baki ɗaya, ba Najeriya kaɗai ba.

A sanarwar da ya wallafa a Facebook, Shugaban Kenya ya ce:

"Rasuwar Buhari ba rashi ne na Najeriya kaɗai ba, har ma da nahiyar Afirka wadda ta amfana da hikimarsa da jajircewarsa wajen ƙwato ƴanci ga al'umma."

Kara karanta wannan

Shin ya kamata ƴan Najeriya su yafewa Buhari? Sheikh Aminu Daurawa ya roƙi abubuwa 2

8. Shugabar Tanzania, Samia Salihu Hassan

Samia Salihu Hassan, shugabar ƙasa mace ta farko a Tanzaniya ta jajantawa Najeriya bisa rashin Shugaba Muhammadu Buhari.

"Ina matuƙar bakin ciki da rasuwar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, a madadin al'ummar Tanzania ina miƙa sakon ta'aziyyarmu."

9. Shugaban Burkina Faso ya yi ta'aziyya

Shugaban soji na ƙasar Burkina Faso, Kaftin Ibrahim Traore ya yi alhinin rasuwar Buhari, inda ya bayyana shi da tsohon soja da ya yi aiki domin ci gaban ƙasarsa.

"Ina miƙa ta'aziyya a madadina da al'ummar Burkina Faso ga Najeriya da iyalan Marigayi Buhari. Ina jinjinawa rayuwar tsohon soja, wanda ya yi aiki domin ci gaban ƙasarsa."

- Inji Kaftin Traore a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.

10. Shugaban Senegal ya yi jimamin Buhari

Shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal ya bi sahun takwarorinsa na duniya wajen miƙa sakon ta'aziyyar Buhari.

A saƙon da ya wallafa a shafin Facebook, Shugaba Faye ya ce:

Kara karanta wannan

Mufti Menk ya yi ta'aziyyar Buhari, ya tuna ɗabi'arsa game da Sallah

"Senegal na jinjinawa da tunawa da rayuwar siyasar fitaccen ɗan Najeriya kuma ɗan Afirka mai kishi. Ina miƙa ta'aziyya ga Shugaba Bola Tinubu, iyalan Buhari da ƴan uwanmu ƴan Najeriya."
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Ana ci gaba da shirye shirye birne Buhari a Daura Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Getty Images

11. Tsohon Shugabam Liberia ya yi alhini

Tsohon shugaban Liberia, George Weah ya yi ta'aziyar rasuwar Buhari, inda ya tuna gudummuwar da ya ba ƙasarsa wajen sake gina dimokuraɗiyya.

A shafinsa na X, tsohon shugaban, wanda ya yi zamani ɗaya da Buhari, ya ce:

"Rasuwar tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, abin alhini ne matuƙa. Bayan nasara a 2015, ya zama ginshikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka, hakan ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya.
"A ƙarƙashin jagorancinsa, Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Liberia a 2017, inda ya bada gudunmawa mai yawa wajen sake gina ƙasarmu.
"Ina tuna lokutan haɗuwarmu, a matakin ƙasashen biyu da kuma na ƙasa da ƙasa. Ya kasance abokin hulɗa na gari a farfaɗowar Liberia."

Bola Tinubu ya naɗa kwamitin jana'izar Buhari

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kwamitin shirya jana'izar Marigayi Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda Buhari ya tsira bayan yunkurin kashe shi a 2014

Bola Tinubu kafa wannan kwamiti da ya kunshi ministoci 10 domin shiryawa da kuma tsara jana’izar ƙasa ta musamman ga Buhari.

Tinubu ya umarci dukkan Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati (MDAs) su buɗe litattafan ta’aziyya a ƙofofin ofisoshinsu domin bai wa jama’a damar yin jaje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262