El Rufai Ya Yi Alhinin Rasuwar Buhari, Ya Fadi Halascin da Ya Yi Masa

El Rufai Ya Yi Alhinin Rasuwar Buhari, Ya Fadi Halascin da Ya Yi Masa

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi ta'aziyyar rasuwar tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari
  • El-Rufai ya nuna alhininsa kan rasuwar Buhari wanda ya yi bankwana da duniya a wani asibiti da ke birnin Landan
  • Tsohon gwamnan na Kaduna ya yaba da irin gudunmawar da Buhari ya ba shi a tarihin siyasarsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

El-Rufai ya bayyana tsohon shugaban ƙasan a matsayin ubangida kuma jagoransa a siyasa.

El-Rufai ya yi alhinin rasuwar Buhari
El Rufai ya yi ta'aziyyar rasuwar Muhammadu Buhari Hoto: @GarShehu, @elrufai
Source: Twitter

El-Rufai ya yi ta'aziyya kan rasuwar Buhari

El-Rufai ya bayyana hakan ne a cikin saƙon ta’aziyyarsa mai taken "girmamawa ga jagora" wacce ya sanya a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya ce Buhari ya tsaya tsayin daka wajen kare ƙasar nan a lokacin yaƙi da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Rasuwar Buhari: Gwamna Radda ya ayyana ranar hutu a Katsina

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa Buhari ya ba da muhimmiyar gudunmawa wajen cigaban ƙasar nan Najeriya a matsayin jami'in soja, shugaban ƙasa na mulkin soja, da kuma shugaban ƙasa da aka zaɓa ta dimokuraɗiyya.

El-Rufai ya bayyana cewa marigayin ya nuna ƙwarin gwiwa da juriyar rayuwa na musamman, inda ya farfaɗo daga kifar da gwamnatinsa a 1985 zuwa samun nasarar zama shugaban ƙasa da aka zaɓa a 2015.

Me El-Rufai ya ce kan Buhari?

“Ko da yake mutum ne mai yin magana kaɗan, yana da nishadi. Yana da ɗabi'a mai jawo mutane zuwa gare shi, wanda hakan ya sa talakawa ke kallonsa a matsayin abin misali na gaskiya da amana, mutum wanda za a iya dogaro da shi wajen kare muradun jama’a."
“Duk da shan kaye a zaɓuɓɓuka uku da suka gabata, ya tara hangen nesa da kuzari don kafa haɗakar jam’iyyu da ta haifar da jam’iyyar APC a 2013. Daga bisani ya kafa tarihi a Najeriya, inda ya kayar da shugaban ƙasa mai ci a zaɓen 2015."
"Bayan kammala wa’adin mulkinsa na biyu, ya mika mulki cikin nasara ga wanda aka zaɓa. A lokacin ritaya, ya ci gaba da jan hankalin jama’a, inda ya ci gaba da karɓar manyan baƙi daban-daban."

Kara karanta wannan

Gwamna Radɗa ya sanar da wurin da za a yi jana'izar Shugaba Muhammadu Buhari

"Na samu damar yin aiki da shi a jam’iyyar CPC. Ya naɗa ni shugaba a kwamitin sabunta CPC bayan zaɓen 2011. Kwamitinmu ya bayar da shawarar cewa ya zama wajibi a haɗa CPC da jam’iyyar ACN da wasu jam’iyyu kafin zaɓen 2015."
"Shugaba Buhari shi ne jagoran siyasa na. Shi ne ya ƙarfafa min gwiwa wajen shiga takarar gwamna a jihar Kaduna. Ya halarci taron ƙaddamar da kamfen ɗina a watan Nuwamba 2014, kuma ya tsaya tsayin daka tare da ni har muka yi nasara."
"Ina matuƙar godiya da goyon bayan da na samu daga gare shi a lokacin da nake gwamna, da kuma damar da na ke da ita ta kusanci da shi, ko da a lokutan da muka saba ra’ayi kan wasu manufofi."
“Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, Ya kuma ba iyalinsa, musamman uwargidansa Hajiya Aisha Buhari da ƴaƴansa ƙarfin zuciya da haƙuri bisa wannan babban rashi."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya yi ta'aziyyar rasuwar Buhari
El Rufai ya yi jimamin rasuwar Buhari Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Gwamna Radda ya ba da hutu kan rasuwar Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina,.Dikko Umaru Radda ya aba da hutu saboda rasuwar Muhammadu Buhari.

Gwamna Radda ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar da babu aiki a jihar Katsina, inda nan ne mahaifar Buhari.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta caccaki El Rufai, ta fadi abin da zai sa Tinubu ya yi tazarce

Hakazalika ya yi addu'ar Allah Ya ji ƙan tsohon shugaban ƙasan na Najeriya wanda ya rasu a birnin Landan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng