Rasuwar Buhari Ta Taɓa Ndume, Ya Faɗi Wasu Abubuwa da Ya Sani
- Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya bayyana alhini a kan rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
- Ya bayyana tsohon shugaban a matsayin a matsayin ginshiki a rayuwarsa, wanda ya yarda da shi da ba shi goyon baya
- Sanatan ya bayyana marigayi Buhari a matsayin mutum mai saukin kai, gaskiya da rikon amana, tare kiransa da uba na gari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya bayyana alhini da takaici bayan samun labarin rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
An tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasar ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025, a wani asibiti da ke birnin Landan na ƙasar Birtaniya.

Source: Facebook
A sanarawar da ya fitar a ranar Lahadi da aka wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Ali Ndume ya ce Najeriya ta yi babban rashin jagora a kasar nan.
Ndume ya yi ta’aziyyar Buhari
Sanata Ali Ndume, ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu, ya bayyana cewa ya kadu matuka da labarin rasuwar Buhari.
A wata sanarwa da ya wallafa, Ndume ya ce:
“Yau da yamma na samu labarin rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari (GCFR) da tsananin alhini da ba zan iya misaltawa ba.
A wurina, ban rasa shugaba kawai ba, na rasa wani ginshiki a rayuwata — mutum wanda ya yarda da ni, ya kuma ba ni goyon baya a lokuta masu muhimmanci.”
Ndume: ‘Buhari yana da saukin kai’
Sanatan ya bayyana Buhari a matsayin mutum mai saukin kai, gaskiya, da rikon amana, wanda ya kasance tamkar uba da jagora a rayuwarsa.
A cewarsa:
“Marigayin shugaban kasa mutum ne mai daraja sosai — ba don matsayinsa na shugaban kasa kawai ba, sai don yadda yake da saukin kai, tsantsar gaskiya da rikon amana.
Ya kasance mai kishin kasa, wanda sadaukarwarsa ta ba ni ƙarfafa guiwa da kwarin gwiwa.”

Source: Twitter
Ya kara da bayyana cewa akwai dangantaka mai kyau a tsakaninsa da tsohon shugaban.
Ya ce:
“Dangantakarmu ta kasance mai armashi da girmama juna. Wasu ma suna zaton ni Kanuri ne saboda irin yanda muke barkwanci da musayar magana tsakanin al’adun Fulani da Kanuri.”
“Karo na ƙarshe da muka gana shi ne a garinsa na Daura, inda na je na kai masa gaisuwa. Har yanzu nakan tuna dumi, fara’a da hikimomin da ya gaya min a lokacin.”
Ali Ndume ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayi Muhammadu Buhari, tare da sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.
Tsohon shugaban kasa, Buhari ya rasu
A baya, mun wallafa cewa yanzun nan muke samun tabbacin cewa tsohon shugaban kasa na Najeriya, Muhammadu Buhari, ya rasu a wani Landan.
Tsohon shugaban, Buhari, wanda ya jagoranci Najeriya daga 2015 zuwa 2023, ya shafe lokaci yana jinya a birnin London tun bayan saukarsa daga mulki.
Rasuwar Buhari ta haifar da alhini a fadin kasar, inda jama’a daga sassa daban-daban ke aiko da sakonnin ta’aziyya ga iyalansa da gwamnatin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng

