Shugabannin Duniya da Suka Fara Ta'aziyyar Muhammadu Buhari
Bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Landan a ranar Lahadi, shugabannin duniya da fitattun ‘yan siyasa sun fara mika ta'aziyya.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Bayan tabbatar da rasuwar Muhammadu Buhari, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci a sassauta tutocin Najeriya.

Source: Facebook
Tuni dai aka fara mika ta'aziyya daga sassa daban-daban na duniya da ma cikin kasar ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, iyala Buhari da yan Najeriya.
Daga cikin wadanda suka fara mika ta'aziyya akwai:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Amurka ta yi jimamin Buhari
Jakadancin Amurka a Najeriya ya aika da sakon ta’aziyya ga al’ummar kasar nan kan rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A wata sanarwa da suka wallafa a shafinsu na X, suka ce:
“Buhari jagora ne da rayuwarsa ta kasance abar koyi wajen sadaukarwa, da’a, da kuma kokarin dawo da gaskiya da rikon amana a ofishin gwamnati.”
“Daya daga cikin muhimman abubuwan da ya bari shi ne kokarinsa wajen karfafa cibiyoyin dimokuradiyya a Najeriya. Muna tare da iyalansa, masoyansa da duka 'yan Najeriya a wannan lokaci mai cike da alhini.”
2. China ta yi ta'aziyyar Buhari
Gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito cewa ofishin jakadancin kasar China a Najeriya ma ya nuna alhini kan mutuwar Buhari.
A wata sanarwa da suka fitar, suka ce:
“Muna alhini da rashin wannan jagoran kwarai wanda bai gajiya da nuna kishin kasa da hadin kan Najeriya. "
"Ba za mu manta da gudummawar da ya bayar wajen inganta dangantaka tsakanin Najeriya da China ba. Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa da daukacin al’ummar Najeriya.”
3. Firaministan Habasha ya yi jimamin Buhari
Firaministan kasar Habasha, Abiy Ahmed Ali, ya shiga cikin jerin shugabannin Afrika da suka bayyana jimaminsu kan rasuwar tsohon shugaban Najeriya.
A wani sakon da ya fitar, ya ce:
“A madadin gwamnatin da al’ummar Habasha, muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma ga gwamnatin da al’ummar Najeriya. Muna tare da ku a wannan lokaci na bakin ciki.”
4. Buhari: Shugaban Saliyo ya yi ta’aziyya
Shugaban kasar Saliyo kuma shugaban kungiyar ECOWAS mai ci a halin yanzu, Julius Maada Bio, ya bayyana alhinin sa dangane da mutuwar Muhammadu Buhari.
A wani sakon ta'aziyyar, ya ce:
“Na ji matukar bakin ciki da samun labarin rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
“A madadin al’ummar kasar Saliyo, ina mika sakon ta’aziyya ga iyalansa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma daukacin al’ummar Najeriya. Wannan babban rashi ne, kuma muna tare da ku a wannan lokaci mai wuya.”
5. Ta'aziyyar Obasanjo ga iyalan Buhari
A Najeriya, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nuna alhinin sa kan rasuwar Muhammadu Buhari.

Source: Twitter
Ya ce:
“Na yi alhinin samun labarin rasuwar aboki na, dan kishin kasa, kuma abokin aiki.”
“A irin wannan lokaci, kasar nan na bukatar kwarewa da basirar duk wanda ya taba jagoranci domin fuskantar kalubalen da muke ciki. Buhari zai bar gibi mai wuyar cikewa. Allah Ya jikansa da rahma.”

Kara karanta wannan
Bidiyo: Ganin karshe da 'yan Najeriya suka yi wa Buhari, yana tare da Atiku, El-Rufai
6. Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Buhari
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce ya shiga rudani da samun labarin rasuwar Muhammadu Buhari a ranar Lahadi.
Buhari ya rasu a wani asibiti a Landan bayan ya shafe lokaci yana rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Source: Twitter
A cikin wata takarda da ya sa hannu da kansa, Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin dan kasa nagari kuma jagora na kwarai.
Ya ce:
“Ya yi wa Najeriya hidima ba tare da gajiya wa ba a matsayin shugaban soja daga Janairu 1984 zuwa Agusta 1985, da kuma a matsayin shugaban kasa mai dimokuradiyya daga 2015 zuwa 2023. Ayyukansa na cike da kishin kasa, da sadaukarwa wajen ci gaban Najeriya.”
7. Gwamnan Kano ya yi alhinin Buhari
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kaduwa da bakin ciki kan rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya bayyana Buhari a matsayin wanda ya yi rayuwa cike da gaskiya.
Ya ce:
“Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen hidima ga kasa da tsantsar gaskiya da jarumtaka.”
8. Kungiyar CAN ta yi ta’aziyyar Buhari
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Arewa ta bayyana bakin cikinta dangane da rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Fasto Joseph Hayab, ya fitar daga Kaduna a ranar Lahadi, ya bayyana Buhari a matsayin uban kasa.
Ya ce:
“Ko da yake ra’ayi ya bambanta a wasu daga cikin manufofinsa lokacin mulki, ba za a iya musanta kishinsa, da’a da kuma jajircewarsa ga hadin kan kasa ba.”
“Rasuwarsa alama ce ta rufe wani babi mai mahimmanci a tarihin siyasar Najeriya.”
Ana shirya gawar Buhari
A baya, mun wallafa cewa ana ci gaba da shirye-shiryen yadda za a gudanar da jana’izar tsohon shugaban kasa na Najeriya, Muhammadu Buhari.
Iyalai da hadiman Buhari sun tabbatar da rasuwar ne a yammacin ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan, babban birnin kasar Birtaniya.
Garba Shehu, wanda ya kasance babban hadimin Buhari, ya bayyana damuwarsa da alhini kan wannan babban rashi tare da nema masa yafiya.
Asali: Legit.ng


