Buhari Ya Fada wa Sheikh Pantami Sirrin da ba a Sani ba kan Shigar Shi Soja
- Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ya tsere wa aure ta hanyar shiga soja tun bayan kammala makarantar sakandare
- Marigayin ya bayyana hakan ne a wata hira da Sheikh Isa Ali Pantami wanda ya taba zama minista a gwamnatin sa
- Shugaba Buhari ya ce yana matashi ne wani baffan shi ya zo Daura da nufin aurar da shi da ’yar sa, amma ya gudu ya shiga soja
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Katsina – Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana wani ɓangare na tarihin rayuwarsa da ba a saba ji ba a wata hira ta sirri da Farfesa Isa Ali Pantami.
Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya taba zama ministan sadarwa a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bayan rike hukumar NITDA.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan ne a cikin wani bidiyo da Sheikh Isa Ali Pantami ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A hirar da aka yi kafin rasuwar Buhari, ya shaida cewa ya yanke shawarar shiga rundunar sojin Najeriya ne domin kaucewa aure bayan ya kammala makarantar sakandare.
Sirrin shiga soja da Buhari ya fadawa Pantami
Buhari ya bayyana cewa wani daga cikin danginsu wanda yake kani ga mahaifinsa, ya zo gida da niyyar aurar da shi da ‘yar sa, amma sai ya gudu ya bar garin Daura zuwa soji.
A cewar Buhari:
"Dan uwan mahafina ne ya zo Daura, ya same ni a kan hanya, sai ya ce ka kai ni gidan ku. Muna zuwa sai mahaifiyata ta ce wannan da mahaifinka ubansu daya."
Ya ci gaba da cewa bayan jin maganar cewa za a daura masa aure da ‘yar dan uwan mahaifinsa, sai ya tsere ba tare da sanarwa ba, domin shiga aikin soja.
A shekarar 1962 ne Buhari ya shiga rundunar soji bayan horo a Najeriya, inda daga nan ya fara taka rawa a manyan mukamai na soja da gwamnati.
Rayuwar Buhari bayan shiga soja
Bayan shiga soja, Buhari ya samu horo na musamman a kasashe daban-daban ciki har da Indiya da Amurka.
Tsohon shugaban kasar ya taka rawa a yakin Biyafara da yakin Mai Tatsine da sauran hare-haren soja a Arewa da Kudu.

Source: Facebook
Ya taba zama gwamnan tsohuwar jihar Arewa maso Gabas, ministan man fetur a zamanin mulkin soja, da shugaban hukumar PTF da aka kafa a lokacin Janar Sani Abacha.
A shekarar 1983, Buhari ya hau karagar mulki a matsayin shugaban mulkin soja, amma daga baya aka kifar da shi.
Bayan shekara da shekaru, ya sake samun nasara a siyasa, inda ya lashe zaben shugaban kasa a 2015, ya kuma yi wa’adin mulki har sau biyu.
An rude a Daura bayan rasuwar Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa makwabtan Muhammadu Buhari a Daura sun shiga jimami bayan sanar da rasuwar shi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya a wani asibiti da ke birnin London.
Baya ga jimami a Daura, Mutane da dama a jihar Kaduna da ke kusa da gidan Buhari sun nuna damuwa da alhinin rasuwar shi.
Asali: Legit.ng


